Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa, kokarin ‘yan wasan kungiyar ya fara dawowa bayan nasarar da suka samu a ranar Larabar akan kungiyar Granada a gasar La liga.
Tun farko dai Real Madrid ta bayyana ‘yan wasanni 24 da za su fuskanci Granada a wasan cin kofin La Ligar na ranar Laraba, cikinsu har da Eden Hazard saboda rabon da dan kwallon tawagar Belgium din ya buga wa kungiyar wasa tun raunin da ya yi a karawa da Alabes ranar 28 ga watan Nuwamba.
‘Yan wasan Real Madrid da suka fafata da Granada:
Masu tsaron raga: Thibaut Courtois da Andriy Lunin da kuma Diego Altube.
Masu tsaron baya: Dani Carbajal da Eder Militao da Sergio Ramos da Raphael Barane da Nacho Fernandez da Marcelo da Albaro Odriozola da kuma Ferland Mendy.
Masu cin kwallaye: Eden Hazard da Karim Benzema da Marco Asensio da Lucas Bazkuez da Luka Jobic da Binicius Junior da Mariano Diaz da kuma Rodrygo Goes.
Sai dai Real Madrid ta buga karawar ta ranar Laraba ba tare da dan wasa Luca Modric ba, wanda ya yi rauni a wasan da sukayi nasara a kan Eibar da ci 3-1 ranar Lahadi kuma kawo yanzu Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki iri daya tsakaninta da Atletico Madrid mai jan ragama ita kuwa Granada tana matsayi na bakwai da makinta 21.
Dan wasa Casemiro ne ya fara zurawa kungiyar ta kasar Sipaniya kwallonta ta farko a raga kafin daga baya kuma Karim Benzema, wanda a satin daya gabata Zidane ya ce babu kamarsa a kungiyar ya jefa kwallo ta biyu.