Kokarin Soke Koyar Da Hausa, Larabci Da Addinin Musulunci A Jihar Katsina

Abdurrahman Aliyu 08036954354

 Duk wata kasa a duniya da ta samu cigaba da daukaka, kafin ta kai ga haka sai da ta ratsa wasu hanyoyi da su kai ma ta jagorancin isa ga wannan cigaban da daukakar. Harshen al’umma da addininsu wasu tsani ne na samar da duk wata nasara da al’umma ka iya samu a ko wane mataki. Al’umma ba zata taba cigaba ba sai ta san addininta da kuma harshenta, tarihi ya nu nu cewa, a Duniya kasashen da suka samu cigaba da daukaka duk wadanda su ke amfani da harshen uwa ne a ya yin mu’amullolinsu na kasa a gwamnatance. Duk kasar da ke amfani da harshe wasu mutane a matsayin harshensu alamu ne ke nu na cewa, har yanzu dai suna karkashin mulkin mallaka na waccen al’ummar da suke amfani da harshenta, sai dai salo kawai da aka sake ma mulkin mallakar.

Na kawo wannan shimfidar ne saboda wannan fili a yau ya na son ya yi diba ne kan badakalar daukar malamai 1950 da ta faru a jihar Katsina, domin da a ce wadanda ke da alhakin daukar sun bi doka kuma sun yi koyi da wadanda suka dauki aiki a gwamnatocin baya ko kuma wasu jihohi makwaftansu da hakan bata faru ba.

Kwanakin baya ne na ji sanarwar cewa, gwamnatin tarayya ta na wani shiri wanda zai ba da dama a rika koyar da darussan kimiya da fasaha cikin harsunan gida, ba dan komi ba sai dan, masana sun tabbatar masu da cewa lallai in aka yi haka za a samu cigaba wanda zai kai wannan kasar ga bullewa bisa hanaya mai kyau. Amma wani abun mamaki tun ba a kaddamar da wannan shiri ba, Jihar Katsina da ake ganin ita ce ta farko da za ta ci gajiyar shirin ta fara watsi da duk wani mataki na kaiwar shirin ga nasara.

Wanda ya sa kwamishinar ilimi ta Jihar ta bayar da umurnin cire duk wani wanda ya karanci Harshen Hausa ko Larabci ko kuma Addinin Musulunci da ga cikin Malaman da ake bukata su koyar a makarantun jihar. Duk da cewa su wadannan malaman an yi masu jarabawa an kuma tantance su sannan kuma su na daga cikin malaman da aka gindayawa sharudda suka cika, wato sun kasance ko dai malam da ke koyarwa ta sa kai ne ko kuma malaman wucin gadi, da su ka yi shekaru daga biyar zuwa sama suna koyarwa a makarantun jihar. Amma kwamishinar da wasu mashawartanta wadanda suke dauke da kwalayen kammala makarantu ba ilimin ba suka ce wajibi ne sai an jire wadannan malamai domin jihar Katsina ba su ta ke bukata ba, kuma ba su da wata rawa da za su iya takawa a fannin koyarwa.

Babban abin da ya kamata wadannan mutane su lura da shi, shi ne, idan su basu bukatar su san kansu kuma su san addininsu da harshen da ya fi kowane harshe dakaka a duniya wato larabci, to bai kamata su hana ‘yayan Talakawa su san wannan ba. Domin duk al’umar da bata san harshenta ba da tarihin yadda ta tsiru da al’adunda da kuma adabinta, to shakka babu ta na cikin hadari, uwa uba kuma ace al’umma ta guji koyar da yaranta addinin da shi ne kaso 99% na mazauna jihar. Sanna kuma har zuwa gudanar da wannan rubutu wannan kwamishina ba ta fito ta yi wa al’ummar wannan jiha bayanin da yasa ta ki sanya wadanda suka karanci wadannan darussa ba. Tambayoyi ne birjik ya kamata ace tazo ta amsa, shin wadannan darussa su na da wadattun malamai ne? ko kuwa cikin malaman da za a dauka na cike gurbin ba mai irin wannan darasi da ya mutu ko kuma ya ajiye aiki? Ko kuwa kwangila ce ta amso ta tarwatsa jihar? Ba bu shakka tun hawan wannan mata a matsayin kwamishina ta ilimi ake ta samun koma baya da kuma yin abubuwa bi sa rashin tsari da sanin makamar aiki, duk da cewa an samu nasarar cin sakamakon jarabawa a lokacin nata, amma wannan ba zai zama hanyar da za a ce ta dace da wannan kujera ba domin nakasun da aka samu a fannin ilimi tun daga hawanta kan karagar mulki ya lunka nasarorinta da ta samu kusan sau biyar.

Domin sam bata yi koyi da magabatanta ba wadanda suka rike irin wannan kujera, bani mantawa ta taba ziyartar makarantar Sakandire ta Kambarawa a gabana da aka yi kokarin ta shiga azuzuwa ta ga yadda azuzuwan suka yi cinkoso da kuma rashin abin zama sai taki shiga, asali sai dai kawai ta nufi waje da wani bango na harabar makaranta ya fadi ta diba ta bayarda dammar a gyara shi, amma kemisisi taki shiga aji saboda tasan da matsalar amma ba wani mataki ko da na ban hakuri ne da shawarar yadda za a magance wannan matsala.

Idan muka koma bangaren koyo da koayarwa sam ba bu wani salo ko shiri na inganta fannin da ta kawo wanda za a ce tsarinta ne, Kai hatta Mai girma gwamana ya fi wannan matar kai ziyarce-ziyarce a makarantu domin diba halin da suke ciki, a matsayin ta na kwamishina ya na da kyau ta gane cewa, akwai wasu nauyi da ke rataye kanta wadanda suke wajibi ta cika su ba wai ta zauna sai daukar hotuna da washe baki ba.

Kiran da wannan fili zai yi ga kwamishinar Ilimi ta jihar Katsain shi ne, a bangaren daukar malamai da ta soke daukar masu wadannan darussa to ta sani masu wannan darussasu ne mafi rinjaye a duk makarantun da ke jihar Katsina. Misali irin su Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarraya da Kwalejin Ilimi Ta Isah Kaita da Kwalejin Koyan shari’a da Sauran Kwasoshi ta Daura da Jami’ar Umaru Musa da Jami’ar Al-Kalam da sauran manyan makarantun da ke jihar, duk wadannan darussa uku da ta tsana su ne ke jagorancin dalibai masu rinjaye a wannan jihar.

Haka ma in aka koma bangaren makarantun sakandire a duk shiyoyi uku da ke akwai a jihar, akwai makarantun sakandire na koyan harshen Larabci. Don haka, yana da kyau wannan kwamishina ta yi koyi da sauran jihohi da suke ba wadannan darussa muhimmanci ita ma ta ba su muhimmanci kuma ta daina kokrin soke wadannan darussa domin duk al’ummar da ke son cigaba sai ta yi amfani da harshen ta da kuma addininta, kuma duk wani ilimi da take tutiyar ta yi daga harshen larabci tsatsonsa ya ke.

Sannan kuma ya na da kyau ta yi amfani da ilimta ba wai kwalinta ba wajen zartar da hukunci, domin sau da yawa ana samun mutum ya na da wani babban kwali a wani bangare, amma kuma ka same shi bai da ilimi na bangaren ko kuma bai san abin da zai yi ba kan harkar tafiyar da mulki. A matsayinki na malamar da ta koyar da Darasin din bai daya a jimi’a (General Studies) to in za ki yi abu ki rika yi bai daya domin shi ne zai kai ki ga mafita da kuma kara kima ta martaba a gwamnatinku. Saboda shi gwamna ba zai iya cewa, komi sai ya yi da kansa ba ku ne ya nada wadanda zaku rike amanarsa kuma ku lurammai da bangaren da ya baku rikon.

Sannan ya na da kyau kwamishina ta rika ko yi da malamta magabatanta domin ba haka suka koyar da ita ba. Sannan wannan fili na kira ga kwamishina da in takardar mai martaba sarkin Katsina ta zo hannunta kan wannan kwamacala da ta yi to ta yi mata karatun ta natsu ta kuma dubi abubuwanda ya rabuto mata a ciki, domin ziyarar da Kungiya marubuta ta kasa ta kai mashi a fadar shi ranar Alhamis 5/10/2017 ya tabbatar wa ‘yan kungiyar da cewa ya rubuta takarda zai aikawa mai girma gwamna kan wannan abu da ya faru, kuma ya umurci wadanda suka kai ziyarar da su zama jakadojinshi kan tabbatar da wanzuwar koyar da harshen Hausa da Larabci da Kuma Addinin Musulunci a jihar Katsina domin su ba za su iya yarda su ba, ta hanyar koyar da su ne kawai jihar Katsina zata taka kowane irin mataki na kololuwar cigaba.

Sannan wannan fili na kira ga kwamishina da ta fitar da duk wani abu ta je ta kalli tsarin da kwamishinonin ilimi na jihar Legas da Kaduna suka yi a bangaren ciyar da harshen gida gaba, daga karshe kuma lallai ya kamata kwamishina ta koma Tarihi ta binciki yadda kasar Hausa ta ginu, ta sani cewa ko kafin Turawa su zo babu abin da ba bu a kasar Hausa, har irin bangaren da ta karanta a kwai kwararru a fanni don haka ilimin boko tsura da take son dabbakawa ta makaro, saboda ko wadanda suka kawo shi sai da suka hada da koyar da Larabci da addinin Musulunci a Makarantun boko na farko da aka samar a Arewacin kasar nan, ya na da kyau ta je ta diba litattafan tarihi ta kara Ilimi ko kuma ta je ta yi babbar Diploma a kan tarihin Ko kan harshen Hausa,, dan ta fita daga cikin gurguwar fahimtar da ta yi wa wadannan darussa. Yanzu dai wannan kwamishina ta an dauke ta saboda haka, wannan fili na kira ga wadanda za su shirya  daukar malaman S-Power da su kula su gyara kuskuren da ta yi ba ya. Ko ba komi dai Hausawa sun ce “Bin na gaba bin Allah”.

Exit mobile version