Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Kokarin Zamanantar Da Makarantun Tsangaya

by Sulaiman Ibrahim
February 13, 2021
in RAHOTANNI
4 min read
Kokarin Zamanantar Da Makarantun Tsangaya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Abin a yaba ne dangane da yunkurin da wasu daga cikin gwamnatocin Nijeriya ke yi wajen bunkasa ilimin makarantun tsangaya, musamman a arewacin Nijeriya, wanda shi ne tsarin ilimin da yafi shahara a bangaren, tare da kasancewa mafi kusa ga karbuwa ga kaso mai yawa a yankin. Wannan yunkuri ne wanda ya dace kuma zai taimaka wajen farfado da ci gaban ilimin yankin.

Bugu da kari, kasancewar sa karbabbe ga mafi yawan mazauna yankin, idan an bunkasa shi zai bayar da mafita wajen rage yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta tare da bayar da gagarumin ci gaba ta fannin ilimi, a matsayin hasken rayuwar kowace al’umma.

An sha kai ruwa rana tare da nuna yatsa a goshin gwamnonin arewacin Nijeriya tare da manyan yan siyasar yankin, a halayyar nuna ko-in-kula a koma bayan lamurran da suka shafi wannan yankin; lamarin da ya hada da kasa gudanar da makarantun tsangaya da almajirci.

Wanda idan mun duba batun da idon basira zai fahimci akwai sakaci da halin ko’in kula da gwamnatocin arewa ke nuna wa da kasala wajen sauke nauyin da ya rataya bisa wuyan su. Yayin da yanzu lokaci ya yi wanda za su dauki matakan gaggawa wajen farfado da tsarin gudanar da makarantun, wanda hakan zai taimaka wajen rage yawan miliyoyin kananan yara da ke gararamba a kan titunan mu- wadanda iyaye suka yiwa jifar matatar mage.

A gefe guda kuma, tuni wasu kasashe sun yi nisa dangane da sha’anin kyautata irin wannan tsarin, wanda kuma a bisa hakikanin gaskiya, wannan tsarin tsangaya da yake gudana yanzu (ta hanyar rashin tallafin gwamnati) a kasar nan, yana taimaka wa wajen dakushe basirar yara da dama tare da kishiyantar ci gaba a jihohin arewacin Nijeriya.

Ilimin All-kur’ani Maigirma da sauran ilmukan addinin musulunci, babban makami ne wajen yakar munanan dabi’u da dakile ayyukan assha, kuma kafa ce ta samar da nagartattu, hazikan mutane wadanda zasu bayar da gagarumar gudumawa wajen gina ci gaban kasa, zaman lafiya da fahimtar juna. Wanda kyautata wadannan makarantun, ta hanyar basu cikakkar kulawar da yakamata, suna daga cikin tushen samar da ayarin mutanen da kowacce kasa zata yi alfahari dasu.

Idan har gwamnatoci da gaske suke yi, wajen kokarin yaki da matsalar tsaro, yaki da matsalar cin hanci da rashawa tare da magance rikicin makiyaya da manoma da makamantan su, wadannan makarantun zasu taka muhimmiyar rawa wajen rage tsaurin wadannan matsaloli, ta hanyar ilimin.

A lokacin gwamnatin Dakta Goodluck Jonathan ta yi rawar gani wajen kokarin gina makarantun tsangaya a daukwacin arewacin Nijeriya. Amma abin kaico shi ne, gwamnonin arewa tare da masu fada a ji, sun ki aiwatar da wannan sabon tsarin farfado da wadannan makarantun, wanda jama’a da dama ke tambayar neman dalilin yin biris da su, alhalin an ware makudan kudade wajen gina su.

Mista Jonathan ya yi wannan yunkuri ne domin rage yawan adadin wadanda basu samu damar zuwa makarantun zamani ba, a arewacin Nijeriya. Wanda gwamnatin sa ta kuduri aniyar kirkiro makarantun tsangaya na zamani- domin farfado da tsohon tsarin ya tafi kafada da kafaca da zamani, a shekarar 2012.

Yayin da tsohon shugaban kasar ya kaddamar da wannan shirin a Sakkwato; ranar 10 ga watan Afirilun 2012 a kauyen Gagi, inda ya yiwa yara dalibai kimanin 25 rijista da hannun sa a wannan sabuwar makarantar tsangaya ta kwana, mai dauke da kayan makarantu na zamani.

Bugu da kari kuma, wannan makarantar, ita ce cikon ta 400 wandanda za a kashe naira biliyan 15 domin gina su a jihohin arewacin Nijeriya.

Haka zalika kuma, zancen da ake yanzu, gwamnatocin sun sa kafa sun yi fatali da aiwatar da tsarin- wanda an riga an dora harsashe, saura shi ne ci gaba. Amma abin ka da wadannan mutanen, akwai yuwar a haka zasu lalace saboda tsabar keta da rashin sanin ciwon kai.

Har wala yau kuma, babu wanda za a dora wa nauyin koma baya da tabarbarewar makarantun tsangaya da almajirci, face shugabanin arewa- na dauri da yanzu. Saboda yadda su Allah ya damka wa amanar al’umma kuma dukiyar kasa; hakkin kowanne dan kasa ta hannun su yake zuwa, amma sun yi kunnen uwar shegu wajen aiwatar da ci gaban yankin, kawai aljihunan su suka sani.

Duk da hakan, kofar tuban wannan zunubi a bude take, saboda haka shugabanin yankin arewa su zabura, bai kamata su ci gaba da zuba ido, wajen sake maimaita kusakuran da suka yi a baya ba- wanda kuma wankin hula yana iya kai mu dare.

Musamman dole su yaba da wannan namijin kokarin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi na gina makarantun tsangaya a arewacin Nijeriya, ta hanyar yin amfani da sabbin makarantun wajen tsugunnar da wadannan aajirai tare da alarammomin su- baya ga kyautata tsarin, wanda kuma idan ba haka ba, za mu dora laifin bisa ga wuyan gwamnonin arewa. Duk da a wasu jihohin, tuni har an karkata akalar makarantun zuwa wani abu na daban, wanda hakan bai dace ba.

Kafin kaiwa wannan gabar, masana a kasar nan sun sha ankarar da yan siyasar arewa da masu rike da madafun iko dangane da babban kalubalen da ke tunkarar su; idan suka yi gigin zura ido a sha’anin farfado da makarantun tsangayar, wajen dawo dasu a karkashin kulawar su. Sannan da jan kunne kan cewa, daya daga cikin abinda ke ci gaba da dakushen yankin shi ne kin daukar fannin da muhimmanci, wanda kyautata shi zai bayar da armashi mai ma’ana ga al’umma.

Wanda kamata ya yi gwamnonin arewa su gudanar da taron tattauna wa a tsakanin su don cimma matsaya guda wajen nemo tudun dafawa dangane da baki dayan matsalar.

Su samar da tsarin bai-daya, su dauki matakin samar da ingantaccen tsari, abubuwan da wadannan makarantun ke da bukatar sa a zamanance, a yanka wa Alarammomin isasshen albashi, a rika baiwa almajiran abinci kyauta tare da basu wata kwarewa da horo na musamman domin amfanar da kan su da al’umma baki daya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Makarantun Islamiyya Sun Samu Tallafi A Katsina

Next Post

NIS Ta Bude Asibitin Jami’anta A Kan Iyakar Kasa Na Gurin

RelatedPosts

ACF

Kungiyar ACF Da Badakalar Jagoranci A Yankin Arewa

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Zailani Bappa, Al’ummar Arewa da dama za su tabbatar...

NLC

Mafi Karancin Albashi: Wata Kungiya Ta Yi Tir Da Kalaman NLC Akan Dan Majalisa Datti Babawo

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Bello Hamza, Wata kungiya mai zaman kanta mai suna...

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Next Post
NIS Ta Bude Asibitin Jami’anta A Kan Iyakar Kasa Na Gurin

NIS Ta Bude Asibitin Jami’anta A Kan Iyakar Kasa Na Gurin

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version