Komai Nisan Dare Gari Zai Waye
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Komai Nisan Dare Gari Zai Waye

byCGTN Hausa and Sulaiman
2 weeks ago
Dare

Ku gafarce mu a sabili da yadda kwamitin sulhu ya kasa ceton yaran Gaza, kuma ya kasa kare mata da tsoffi da likitoci da nas nas da ‘yan jarida a Gaza…Kasashe mambobi 14 na kwamitin sun yi namijin kokari, amma sun kasa samar da taimako, sakamakon yadda Isra’ila ke samun kariya daga tsarin duniya maras daidaito. Kalaman da zaunannen wakilin kasar Aljeriya a MDD Amar Bendjama ya yi ke nan a jawabinsa, bayan da kasar Amurka ta sake kada kuri’ar rashin amincewa da wani daftarin kudurin tsagaita bude wuta a zirin Gaza a taron kwamitin sulhun da ya gudana kwanan nan, inda Mr. Amar Bendjama ya yi ta rokon gafara har sau 11.

A ranar 18 ne, kwamitin sulhun MDD ya kada kuri’a a kan wani daftarin shiri da ya bukaci a dakatar da bude wuta a Gaza nan da nan ba tare da sharuda ba, daga cikin kasashe mambobi 15 na kwamitin, 14 ne suka kada kuri’ar nuna amincewa, a yayin da kasar Amurka wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin ta hau kujerar na ki, matakin da ya sa aka kasa zartas da kudurin. Hakan kuma ya kasance karo na shida da Amurka ta kada kuri’ar rashin amincewa da irin kudurin a kwamitin sulhun.

A jawabin da ya gabatar bayan kada kuri’ar, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mr. Fu Cong ya yi tambayoyi guda uku game da yadda Amurka ta hau kujerar na ki yadda ta ga dama, wato asarorin rayuka nawa ne za su kai ga tsagaita bude wuta a Gaza? Sa’an nan, aukuwar masifofi nawa za su kai ga shigar da kayayyakin jin kai Gaza ba tare da matsala ba? Sai kuma zuwa yaushe ne kwamitin sulhu zai kai ga gudanar da aikin da ya wajaba?

Shekaru kusan biyu ke nan da barkewar rikici a Gaza, rikicin da ya haifar da mummunan yanayin jin kai. Kwamitin sulhun ya yi ta yin kokari, amma Amurka ta zama karfen kafa ta hana. Idan ba mu manta ba, karon farko da Amurka ta kada kuri’ar rashin amincewa a watan Oktoban shekarar 2023, rikicin ya halaka mutane kusan 3000. A lokacin da Amurka ta sake kada kuri’ar a wannan karo, adadin mamata a sanadin rikicin ya karu har zuwa sama da dubu 65.

MDD da aka kafa bayan yakin duniya na biyu a kimanin shekaru 80 da suka gabata, yana daukar burin bai daya na bil Adam game da wanzar da zaman lafiya da ci gaba a duniya, wadda ta bude sabon babin tsarin jagorancin duniya a lokacin. Amma yadda Amurka ta hana kwamitin sulhu daukar matakai da kuma kare aniyarta ta kare aikace-aikacen da suka saba wa kudurin kwamitin sulhu, ya sa kwamitin sulhun gaza taka rawar gani a kan batun Gaza. Taron da aka gudanar a wannan karo ya kasance na 10,000 ga kwamitin sulhun, wanda ya kamata ya zama sabon babin MDD na kiyaye zaman lafiya a duniya, amma a maimakon haka, kuri’ar da Amurka ta kada ta tono mana matsalolin da MDD ke fuskanta ta fannin tsarin jagorancin duniya.

Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar matakai na kashin kai, tare da kiyaye matsayin MDD, don ta taka rawar da ba wanda zai iya maye gurbinta a cikin tsarin jagorancin duniya. Lallai kasar Sin ta gabatar da shawarar, musamman don neman dakile ayyukan nuna fin karfi da ake fama da su a duniya, tare da samar da mafita ga kasa da kasa da suka shiga duhu.

A sati mai zuwa, za a gudanar da babbar muhawara da ma babban taron tabbatar da shirin samar da kasashe biyu a yayin babban zauren MDD, kafin haka, manyan kawayen Amurka irinsu Birtaniya da Faransa cewa suka yi za su amince da kafuwar kasar Palasdinu, lamarin da ya sake shaida cewa, babu wanda zai iya hana adalci. Lokacin da Amurka ta kada kuri’ar nuna rashin amincewa, ba yarjejeniyar zaman lafiya kadai ta jefa cikin kwadon shara ba, har da matsayinta na jagorancin duniya.

Tabbas “komai nisan dare gare zai waye”, duk duhun da Gaza ke ciki, haske zai bayyana. Fatan kasa da kasa na wanzar da zaman lafiya zai kai ga kawar da dukkan abubuwan da ke tarnaki tare da shimfida dauwamammen zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, wanda hakan zai bude mana sabon babin tsarin jagorancin duniya.

 

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Next Post
SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook

SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version