Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Korar Tuchel Za Ta Iya Hana Mbappe Komawa Real Madrid

by Muhammad
December 26, 2020
in LABARAI
1 min read
Tuchel
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa korar da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yiwa kociyan kungiyar Thomas Tuchel zata iya hana dan wasa Kylian Mbappe komawa Real Madrid a karshen kakar wasa.

A ranar Alhamis ne kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kori Thomas Tuchel, dan asalin kasar Jamus sanarwar da akasarin kafafen yada labaran Faransa dana nahiyar turai suka yi ta yadawa   ta tabbata.

samndaads

Thomas Tuchel na daga cikin mutanen da suka taimakawa kungiyar ta PSG tsawon lokacin da ya share da babbar kungiyar PSG kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar tun bayan komawarsa daga kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus.

Rashin lashe kofin zakarun Turai ya sa magabatan kungiyar ta PSG suka yanke shawarar korar Tuchel bugu da kari a wannan kakar wasan kungiyar bata buga abin arziki a gasar lig one ta kasar Faransa kuma tuni kungiyar ta shiga tattaunawa da wani makusancin Tuchel, dan kasar Argentina Mauricio Pochettino.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi alkawarin sayan dan wasa Mbappe idan an kammala kakar wasan bana wanda hakan ne yasa kungiyar bat sayi dan wasa ko daya ba a kasuwar data gabata saboda tana tara kudin sayan Mbappe.

A kwanakin baya dan wasan shima ya bayyana cewa bashi da burin ci gaba da zaman kungiyar kuma yana fatan a karshen kakar wasa zai koma daya daga cikin kungiyoyi manya a nahiyar turai.

SendShareTweetShare
Previous Post

Zulum Ya Nemi Kiristoci Da Su Yi Addu’a Ga Sojoji, ‘Yan Banga Da Sauransu

Next Post

Na Gama Shirin Fafatawa Da Tyson Fury -Anthony Joshua

RelatedPosts

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

by Yahuzajere
11 mins ago
0

A kokarinta na tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan, Hukumar...

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

by Daurawa Daurawa
3 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Rahotonnin da suke fitowa daga fadar...

Tattabaru

Abin DaYa Sa Tattabarun Da Buhari Ya Saki Ba Su Tashi Ba – Adesina

by Muhammad
4 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa...

Next Post
Joshua

Na Gama Shirin Fafatawa Da Tyson Fury -Anthony Joshua

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version