Korea ta Arewa Zata tattaunawa kai tsaye da Korea ta Kudu

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya gayyaci takwaransa na Korea da Kudu Moon Jae-in don tattaunawa a babban birnin kasarsa, Pyongyang.

Karo na farko kenan cikin sama da shekaru 10, da shugabannin kasashen biyu, zasu gana kai tsaye.

Kanwar shugaban Korea ta Arewa Kim Yo Jong ce ta mika sakon gayyatar tattaunawar da baki, a lokacin da tawagar Korea ta Arewan ta ke ganawa da shugaban Korea ta Kudu Moon Jae-in fadar gwamnatinsa.

A ranar Juma’a ne dai aka fara gasar Olympics ta hunturu a Korea ta Kudu, wadda ‘yan wasan korea ta Arewa ke halarta, duk da cewa ba’a ware-ware matsalar diflomasiya tsakanin bangarorin biyu ba, wadda ta samo asali a dalilin shirin Korea ta arewan na mallakar makaman nukiliya.

 

Exit mobile version