Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Addu’a Ce Mafita, Ba Kulle Mutane Ba – Wakilin Dukiya

Published

on

An bayyana cewa kulle kasarnan da hukumomi tun daga matakin kasa har zuwa jiha da suka yi bai yi daidai ba.Wani dattijon dan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya shiya bayyana hakan.
Ya yi nuni da cewa a kulle mutum bashida abinda zaici ko kuma a kulle mutane samada 10 a dauko abinci da bai wuce na mutum uku ba a basu ace shi za su ci ba inda zai kai face wahala da kara faruwar abubuwa marasa dadi.
Alhaji Yusuf ya yi nuni da cewa yanzu gashi abubuwa sun tashi sunyi tsada sun nunnunka a sakamakon wannan kullewar kuma ya akaji da halin dama da ake ciki da dama ana neman tak ne mai neman kuka aka jefeshi da kashin awaki sai ya yi kuka amma gaskiyar magana tsakani da Allah Gwamnati yakamata ta yi adalci ta nuna ranar kiyama Allah zai tambayeta yanda ta gudanarda mu’amalarta mutane suna cikin yunwa da masifa da talauci da fatara ga karancin wuta ga zafi ana fama dashi duk a kasarnan.
Alhaji Yusuf Ibrahim wanda dan kasuwar musayar kudi ne a jihar ta wapa a jihar Kano kuma tsohon shugaban kungiyar kasuwar ya kara da cewa abin da yakamata Gwamnati ta ce a yi shi ne addu’a ba a kulle mutane ba. Addu’a ita ce abin da za’a rika dan kwaranye wannan masifa.
Ya yi nuni da cewa amma an kulle mutane sunata kunkuni suna Allah ya isa an hanasu yin ibadarsu.Wanda kin yin Sallar nan a jam’i ba karamar tashin hankali bane a kasarnan balle kasar Saudiyya da suka ki yi suma sun gano cewa masifa ce ba kadan ba saboda haka tunda Damakwaradiyya ake yi abar kowa ya yi addininsa ya yi ibadarsa mu roki Allah ya kwaranye wannan masifa da bala’i domin mutane su na cikin masifa sai dai a roki Allah su kuma hukuma su duba jagoranci da Allah ya ba su su ga yaya za su yi kuma addu’a ita ce mafita su fito su roki Allah jama’a su roki Allah shi ne mafita.
Ya ce, ana maganar Korona to mace-mace da ake ai ba kurona bace annoba ce ita kuma annoba shahada ce ga musulmi wanda suka mutu Allah ya karbi shahadarsu wanda suke anan Allah ya basu lafiya.
Alhaji Yusuf Ibrahin wakilin Dukiya ya ce, a kasarnan bamuda cigaban da za mu kulle mutane Gwamnati bata da abin da za ta bai wa mutane maganace ta abinci da ruwansha ba mu da shi. Da Allah ya sa mu na da shi ai wadanda suka kulle ai sun kulle ka dubi kasar Saudiyya yanda suke ajiyewa mutum kayan abinci a kofar gida yanzu sun bude sunce kowa ya fita yaje ya nemi abinci saboda yau da kullum.sai Allah ba wanda ya isa ya tsaya maka yau da kullum yakamata hukuma ta tsaya ta duba taji tausayi danta inganta rayuwar al’umma.
Advertisement

labarai