Umar A Hunkuyi" />

Korona: Akwai Yiwuwar Mutuwar Masu Fama Da Tarin Fuka Miliyan Daya

Akwai yiwuwar mutuwar akalla masu fama da cutar tarin fuka miliyan guda, a kuma inda yake da yiwuwar mutane sama da miliyan 6.5 su yi fama da cutar a fadin Duniya a zango na biyu na annobar Korona.

Hakan na zuwa ne a bisa yanda hankalin masu kula da cutuka da bayar da magani a Duniyar nan a halin yanzun ya fi karkata a kan annobar ta korona a bisa sauran cutukan da al’ummomi suke fama da su kamar yin allurorin magani da na rigakafi kan cutar ta tarin fuka da makamantansu.

Sabon babban daraktan gadauniyar kula da masu fama da tarin fuka ta, KNCB Tuberculosis Foundation, Dakta Mustapha Gidado, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, ga manema labarai.

Gidado, wanda shi ne kwararre na farko wanda ba dan kasar Jamus ba da ya riki wannan mukamin, ya kuma bayyana cewa, tilas ne a saukake magungunan cutar ta tarin fuka ta yanda za ta bayar da sakamako mai kyau na gano dukkanin matsalolinta.

A cewarsa: “A yanzun haka muna cikin wani irin mawuyacin hali ne na fama da annobar Korona a duk fadin Duniya, a inda a yanzun haka sama da mutane miliyan 20 suka kamu da cutar. Tabbas a halin yanzun muna dumfara lokaci ne na fara kwasan miliyoyin gawarwaki, wanda wannan babban abin takaici ne da ba a yi tsammaninsa ba.

“Matsalar annobar korona da ta tarin fuka ta nemi ta sha karfin masana. Sanayya da abin da ke faruwa a yanzun haka sun nuna kokarin da ake yi na magance annobar yaduwar korona, abin takaici ya zo da hanyoyin lalata wasu ayyukan lafiya da suka shafi sauran cutukan.

“An kiyasta sama da masu fama da cutar ta tarin fuka miliyan 6.5 za su kamu da annobar a nan ba da jimawa ba, sannan abin takaicin shi ne akwai yiwuwar a wani lokaci nan gaba kadan za mu fara kwasan miliyoyin gawarwaki ne kawai. Duk kuma a sabili da matsalar annobar ta korona da kuma lalacewar tsarin lafiya na Duniya bakidaya.

“Amma annobar ta korona, duk da cewa tana wa harkar tsarin lafiyarmu illa a kan sauran cutukan da ake fama da su, amma abin da muke tunani muka kuma yi amanna da shi, shi ne za mu kuma iya cin gajiyar  irin tanadin da muka yi wa ita annobar ta korona domin tallafa wa ainihin sashen na lafiya a kan sauran cutukan da suka hada da na tarin fuka.

Ya kara da cewa: “A yanzun haka, in har ba mu iya yin taka-tsantsan ba, mutanan da suke fama da korona za su tsorata da zuwa wuraren neman magani domin ka da a ce suna fama ne da tarin fuka ko akasin hakan.

“Wasu mutanan da suke fama da matsalolin numfashi wadanda zai iya kasancewa na tarin fuka ne, zai yiwu su ki zuwa wuraren neman magani domin a duba matsalarsu tun da wuri ko a gano korona a tare da su a dora su bisa magani a kan lokaci.

“Korona ta yi wa kokarin magance tarin fuka illa ta kowace fuska. Daya daa cikinsu shi ne ta lalata tsarin lafiya da ake tafiya a kansa saboda a halin yanzun kusan kowa hankalinsa ya koma ne a kan neman maganin annobar ta korona.

“Don haka, ba tarin fuka ne kadai ya gamu da matsalar korona ba, sauran sassan lafiya duk su ma a yanzun haka suna fama da matsalar ta korona, kama daga allurorin rigakafi, sashen kula da mata masu ciki da sauran sassan lafiya har da na masu fama da cutar sukari.

“Bincikenmu na baya-bayan nan a kan matsalar da korona ta haifar wa tarin fuka ya nu na an samu ragowa matuka na yawan mutanan da suke zuwa domin kokawa da tarin fuka din, wadanda da ma can suna a kan magani ne, a yanzun haka suna samun matsala domin ba sa iya samun damar ci gaba da karbar maganinsu.

“Sai dai, kasashe da yawa suna ta zuwa da wasu hanyyi na magance wannan matsalar. Hukumar lafiya ta Duniya ta ba mu wasu hanyoyin na irin wadannan kasashen domin tabbatar da ba a lalata hanyoyin kula da lafiya na masu fama da tarin guka ba a dalilin annobar korona.

“Abu na farko da muke da bukatar yi shi ne, sanin su waye wadannan majinyatan da ba a san da su ba, a ina suke, wane irin taimako suke da bukata, ta ya kuma za mu iya taimaka masu?”

“Ba zai yiwu mu iya kasancewa a kowane wajen bayar da magani da duba marasa lafiya ba, don haka, tilas ne mu tsara wasu hanyoyin da dubarun da kuma sharuddan domin aikin namu ta yanda za mu iya isa ga kowa.

“Takena a wannan matsayin shi ne, a saukake hanya. In an saukake hanya, sai a rika nunka ta. A wajen kula da tarin fuka, hanya daya da z aka iya bambance ta shi ne in ka yi gwaji ka yi shi a ko’ina. Yin sa a ko’ina ba zai bayar da bambanci a tarin fuka ba,” in ji shi.

 

Exit mobile version