Korona: An Jinjinawa Gwamnatin Tarayya Bisa Sassauta Doka A Abuja, Legas Da Ogun

Dr Joe Okei-Odumakin, shugaban kungiyar ‘Centre for Change,’ ya jinjinawa matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na sassauta dokar garkame garuruwan Legas, Abuja da Ogun.

Okei-Odumakin, ya yi wannan jinjinar ne a ranar Talata a Legas, inda ya ce abin shugaban kasar ya yi abin a yaba masa domin dakatar da komai ya jawo wa bangaren tattalin arziki koma baya.

A daren jiya ne Shugaba Buhari ya sassauta dokar a jihohin Legas, Ogun da kuma Abuja, inda sassaucin zai fara daga 4 ga watan Mayu.

Exit mobile version