Muh'd Shafi'u Saleh" />

Korona: Babu Dalilin Da Zai Sa Mu Kafa Dokar Kulle -Fintiri

Gwamnan Adamawa

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce ba zai sake kafa dokar kulle saboda dalilan annobar korona a jihar Adamawa ba.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne, duk da karuwar masu dauke da cutar da’ake ci gaba da samu yanzu haka a jihar, Fintiri ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Yola.

A satin da ta gabata ne hukumar NCDC ta sanar da mutum 50, da cewa sun kamu da cutar korona, adadi mafi-yawa da’aka taba samu a jihar.

Duk dai yawan adadin ya rago zuwa mutum 26 a bayanan da hukumar ta fitar na ranar 10 ga watan Janairun 2021. Yanzu haka dai jihar na da adadin mutane 494 da ke dauke.

 

Exit mobile version