Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Bankin Fidelity Ya Bai Wa Yobe Tallafin Naira Miliyan Biyar 

Published

on

A nashi bangare domin bayar da tallafi talkafi a kokarin da gwamnatin jihar Yobe take a yaki da yaduwar annobar korona, hukumar gudanarwar reshen Bankin Fidelity a jihar ya bayar da tallafin naira miliyan biyar wajen yaki da annobar a jihar.

Da ya ke karbar tallafin a birnin Damaturu, mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar annobar korona a jihar, Hon. Idi Barde Gubana, ya yaba wa hukumar gudanarwar bankin dangane da tallafin.

Ya ce, “Kwamitin zai aiwatar da wannan tallafin bisa kudurorin yunkurin Gwamna he donation would Hon. Mai Mala Buni a matakan yaki da bazuwar annobar a fadin jihar.”

Haka zalika kuma, shugaban kwamitin ya bukaci sauran takwarorin Bankin Fidelity da sauran kungiyoyi da cewa su yi koyi dashi tare da basu tabbacin cewa tallafin su zai kai ga inda su ka nufa.

A nashi bangaren kuma, a lokacin da yake mika cak din kudin, babban jami’in yanki a Bankin, Dr. Musa Tarinbuka, ya ce tallafin sashe ne na nauyin da ya rataya a wuyan bankin wajen bayar da tasu gudumawa ga duk abinda ya shafi al’ummar jihar Yobe a kokarin da take yi na yaki da annobar korona.

Haka kuma, manajan yankin ya yaba da matakan da gwamnatin jihar take dauka a fannin yaki da yaduwar cutar korona, inda ya sake bayyana cewa Bankin su zai yi duk abinda ya dace wajen bayar da cikakken goyon bayan su ga manufofi tare da kudurorin gwamnatin jihar.

Dr. Tarinbuka ya bayar da tabbacin cewa, bankin su zai ci gaba da hada hannu da gwamnatin jihar a yakin da take da annobar korona tare da sauran cutuka, a fadin jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: