Connect with us

LABARAI

Korona: Bayan Dawo Wa Aiki, Za Mu Koyar Da Membobinmu Daukar Matakan Kariya- ‘Yan Canji

Published

on

Kungiyar ‘yan canji ta Nijeriya, ABCON a ranar Alhamis ta ce tuni ta fara wayar da kan membobinta tare da sanar da su matakan da ya kamata su dauka wajen dakile yaduwar cutar Korona da zarar sun dawo bakin aiki.

Alhaji Aminu Gwadabe, shugaban ABCON shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a Legas, inda ya ce tuni ‘yan canjin ke cikin halin farin cikin kan yadda za a dawo wa bakin aiki da kuma tsarin da CBN ta bullo da shi dangane da ci gaba da canjin kudaden waje.

Ya ci gaba da cewa dokar zaman gida na mako 5 da aka kakaba ya sanya canjin kudaden waje a bakar kasuwa ya yi tashi gwauron zabi, inda yanzu Dala 1 take a naira 450.

Sai dai ya ce bai kamata a ce farashin dala din ya kai haka ba. Ya ce sun ji dadin labarin sassaucin nan da aka samu, kuma za su su ji labarin hakan a tasoshin jiragen sama.

“Ta janibinmu tuni muka shirya daukar matakan kariya da ya hada da rashin tara jama’a da yawa, bada tazara a tsakani, sannan zamu samar da hanyar Intanet da mutane za su rika samun tikitinsu. A shirye muke, mun dauki darasi daga annobar Korona musamman ta fuskacin cunkoson jama’a.” Inji shi.

Sannan ya tabbatar da cewa za su tilasta sanya abin fuska, wanke hannu tare da amfani da na’urar gwajin zafin jiki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: