Korona: Buhari Ya Tsawaita Ayyukan Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Yaki Da Korona

Daga Khalid Idris Doya,

 

Shugaba Muhammadu Buhari, ya sake tsawaita wa’adin kwamitin da ya kafa na yaki da annobar Korona zuwa karshen Maris din 2021 biyo bayan sake kunno kai da cutar ya yi.

A wani sako da shugaban kasa Muhammadu Buharin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba zai yiwu ci gaban da aka samu na watanni tara da suka gabata ya tafi haka nan ba.

Ya ce, “Na tsaya na yi nazari kan lamarin kuma na aminta da cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa wajen dakile yaduwar wannan cutar ta korona.”

Shugaban ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da kuma malamai da su ba kwamitinsa hadin kai wurin wayar da kan al’umma kan cutar.

A shekaran jiya ne dai kwamitin shugaban kasar da ke yaki da korona ya sake bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa kasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

Haka kuma kwamitin ya sanar da rufe dukkanin makarantu da kuma wuraren motsa jiki.

Kwamitin kuma ya saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya dauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake dauka a baya.

Exit mobile version