Connect with us

MANYAN LABARAI

Korona: Buhari Zai Bude Wa Wasu Dalibai Makarantu

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara sassauta dokar kulle da a ke yi a kasar sakamakon dakile Annobar Cutar Korona, inda ta tsara cewa, za ta bude makarantu ga daliban da su ka kusa kammala makarantunsu a cikin zangon na biyar na matakan yaki da cutar, wanda zai fara daga gobe zuwa makonni hudu masu zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, lokacin da ya ke gabatar da taron manema labarai da ya saba gudanarwa, don yi wa ’yan kasar bayanin halin da a ke ciki jiya Litinin, 29 ga Mayu, 2020.

Mustapha ya kara da cewa, wannan zangon kullen zai kama har tsawon makonni hudu, to amma Shugaban kasar ya amince da sassauta dokar tsallakawa zuwa jihohi, inda za ta rika aiki ne kawai a lokutan da a ka ware na hana zirga-zirga, wato daga karfe 10:00 na dare zuwa 4:00 na Asubahi daga gobe Laraba, 1 ga Yuli, 2020.

Ya ce, za a iya bude wa wasu dalibai ajijuwan makarantu ne ta hanyar kiyayewa kuma ga daliban da su ke dab da kammala karatunsu, domin akalla su samu damar gama makaranta.

Shugaban Kwamitin ya kuma kara da cewa, sabon zangon sassaucin na makonni hudu zai fara ne daga yau Talata, 30 ga Yuni, 2020 zuwa 27 ga Yuli, 2020, inda bayan nan gwamnati za ta sake duba yiwuwar daukar wasu matakan.

Sai dai kuma ya yi kashedin cewa, dukkan sauran ka’idoji na cudayya su na nan daram, inda yin amfani da takunkumin baki da hanci da dabbaka dokar nisantar juna, za a cigaba da tabbatar da su a tsakanin al’umma, ya na mai cewa, hakan ya zama dole ne saboda kasancewar har yanzu ba a samu magani ko rigakafin cutar ta Korona ba.

Gabanin taron manema labaran dai, sai da tawagar kwamiti ta fara ganawa da Shugaba Buhari jiyan a Fadar Shugaban kasa, inda bayan hakan ne kuma ’yan tawagar su ka fito, su ka bayyana wa duniya wannan matsayar da su ka dauka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: