Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Korona: CBN Ya Shirya Hada Kai Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu

Published

on

A jiya ne babban bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa, ya shirya tsaf domin hada kai da kamfanoni masu zaman kansu wajen dakile cutar Korona. gwamnatin babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele shi ya bayyana hakan a Jihar Legas wajen bude saban cibiyan killace masu cutar Korona da ke Yaba. Wannan saban cibiyan an samu gine shi ne sakanakon hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, domin yakar cutar Korona.

Da yake gabatar da jawabi wajen bude cibiyar, gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya ce, “bude sabon cibiyar killace mutane zai taimaka wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya a Nijeriya, musammam ma wajen hana yaduwar cutar Korona a Jihar Legas. CBN a shirye yake wajen yin kokarin aiki tukuru tare da kamfanoni masu zaman kansu domin yakar cutar Korona a cikin kasar nan.”

Emefiele ya bayyana cewa, dole ne sai an hada hannu da karfe wajen hana yaduwar cutar Korona, saboda cutar ta raunata tattalin arzikin Duniya musammam ma tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce, “tattalin arzikin Nijeriya ya girgiza matuka, haka kuma an samu matsalolin lafiya da karancin samun kudaden shiga wanda ya kai na kashi 55, sakamakon durkushewar farashin man fetur a kasuwan Duniya tsakanin watan Junairu da watan Mayun shekarar 2020.

“Wannan ne ya sa dukkan gwamnatocin jihohi suka hada kai da kamfanoni masu zaman kansu domin magance matsalolin da rayuwan mutane da kuma farfado da tattalin arzikin kasar nan. Mun aiwatar da mabambantan shirye-shirye wajen magance barnan wannan cuta wadanda suke hada da tallafi biliyan 50 ga magidanta da kananan ‘yan kasuwa wadanda cutar ta dan-danta tattalin arzikinsu da kuma biliyan 100 ga harkokin kiwon lafiya da naira tiriliyan daya ga harkokin noma da kamfanoni masu sarrafa kayayyaki wajen farfado da tattalin arzikinsu.

“kokarinsu shi ne, mu dakile yaduwar wannan cuta domin kare rayukan mutane, wannan ne ya sa dole mu hada hannu da karfe da kamfanoni masu zaman kansu domin magance wannan babban matsalar.”

Bayan haka, ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu wajen hada kai da gwamnati domin bayar da tallafin naira biliyan 29. Za a yi amfani da wadannan kudade wajen gina cibiyoyin lafiya da ke cikin kasar nan.

“Sakamakon gudanar da wannan hadaka tsakanin gwamnati da kamfanini masu zaman kansu, an samu nasarar samar da cibiyoyin killace mutane guda 32 a jihohi 32 da ke fadin kasar nan. Muna kyautata zato daga nan zuwa karshen watan Yuli, za a samar da cibiyoyi 39 a fadin kasar nan,” in ji gwamnan CBN.

Da yake gabatar da jawabi, gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, bude sabon cibiyoyi abun alfahari ne ga ‘yan Nijeriya da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

A cewarsa, “Jihar Legas ta samar da kadaje guda 24,000, yayin da gwamnatin tarayya ta samar da guda 3,000. Za mu iya dakile wannan cuta ce ta hanyar hada hannu da karfe a tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, domin tallafa wa kasar nan.

“A nan Jihar Legas, muna da mutanen da suka kamu da wannan cuta guda 10,000 kuma muna iya kulawa da su. A yanzu haka an sallami maginyata guda 1,500 daga cibiyoyin killace maginyata, a yanzu muna da majinyata guda 5,000, sannan mun samu waadanda suka mutu guda 128. Akwai matsaloli da dama da gwamnatin jiha take fuskanta tare da kokarin bin hanyoyin maganci wadannan matsaloli ta bangaren dakile yaduwar wannan cuta ta Konona.

“Wadannan kayayyakin aiki za su kara ba mu damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Wannan cibiya da muke gani za ta kasance cibiyar gudanar da binciken wannan cuta a Duniya baki daya tare da horar da likitoci, wanda aka samar da ita sakamakon hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Muna godiya ga daukacin mutanen da suka halacci bude wannan cibiya kuma Allah ya kai kowa gidansa lafiya.”

Shugaban gidauniyar Aliko Dangote Foundation (ADF), Aliko Dangote, ya bayyana cewa, wannan sabon cibiyar killace mutane tana daya daga cikin gine-ginen da muke alfari da ita. Dangote wanda ya sami wakilcin babban jami’in gidauniyar ADF, Zouera Youssoufou.

Ya ce, “muna matukan alfahari da wannan cibiya saboda wannan cibiya an samu yi masa gini na zamani kuma muna kokari wajen ganin an gina irin wannan cibiya a ko’ina a cikin jihohin kasar nan.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: