Korona Da Rikicin Manoma Da Fulani Sun Durkusar Da Mu – Mata Manoma

Wata manomiyar Rogo Uwargida Bines Adigizi da uwargida Caroline Abimiku manomiyan Doya da kuma uwargida Jumai Yohanna a kauyen Ikposoge a karamar hukumar Obi cikin Jihar Nasarawa.

A hirarsu mabanbanta da jaridar Nigerian Tribune sun bayyana cewa, tun su na kananan suke yin noma saboda sha’awar da suke da ita ta sana’ar.

A cewar Jumai Yohanna wacce ta kasance Kaka mai jikoki biyu ta kuma horas da daukacin ‘ya’yanta kan aikin noma, inda ta kara da cewa, da ribar da take samu ne take bai wa. ‘ya’yanta da ilimin Boko.

Jumai Yohanna ta koka da cewa, a yanzu ta na fuskantar kalubale rashin lafiya saboda yi asarar amfanin gonar ta da kuma dabbobin ta da kudinsu ya kai na miloyin naira saboda yawan rikice-rikice.

Jumai Yohanna ta ci gaba da cewa, a matsayin ta na mace kuma karamar manomiya, an mayar da mu saniyar ware wajen samun tallafi daga gun gwamnatin, duk da cewa, an samar da tsarin yin raba daidai na bayar da tallafi a tsakanin mata da kuma masa manoma a kasar nan.

“Ina rokonka ba na son ka tabo min bangren irin asarar da na yi, domin zan iya barke wa da kuma kuma asarar, na daya daga cikin abinda ya tayar min da rashin lafiya ta.”

A cewar Jumai Yohanna, “Na kuma nayi asarar Shinkafa, Doya Kankana mai yawa tare da kuma Akuyoyi na.”

Jumai Yohanna har ila yau, a shekarun baya, ta yi asarar dabbobobin ta da kuma amfanin gonar ta a lokacin rikicin Fulani Makiyaya, inda daga baya ta dan farfado ta ci gaba da sana’ar, sai da ta na fuskantar kalubalen samun tallafi domin ta tsaya sosai da wafafun ta.

Jumai Yohanna ta ci gaba da cewa, ta yi kokarin sayen ingantaccen Iri daga gun hukumar bunkasa aikin noma NADP ta jihar Nasarawa, inda ta koka kan cewa, sai dai rashin kudi ya dakile kokarin na ta.

“A wasu lokutan mu na ji ana cewa, gwamnati ta rabar da takin zamani, amma idan mun je can, babu wanda ya ke ba mu kuma iya kokarina domin in samo rancen kudin aikin noma kuma duk da cewa sai na biya wasu kudade amma babu wata nasara, ba zan kara nema ba domin na san, ba zan samu ba.”

Ta kara kuma bayyana cewa, annobar Korona ta kuma kara tabarbarar da sana’ar.

Kamar dai Jumai, sauran mata manoma kanana da sauransu a Nasarawa sun fuskanci kalubalen Na korona musamman a lokacin kulle.

Har ila yau kuma, babban bankin Nijeriya CBN ya kirkiro da bayar da bashin naira biliyan 50 domin amfanin matasa karfi da kuma masu kananan Da matsakaitan sana’oi dak a kasar nan.

Har ila yau, ya kuma samar fa naira tiriliyan daya domin a bunkasa manyan fanonin tattalin arzikin kasar nan ta hanyar bayar da bashi.

An ruwaito cewa a wasu kananan hukumomi, lamarin ya janyo mata manoma da dama, ba su iya samun kayan aikin noma a kan lokaci ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake shirin shiga aikin noma na kakar bana.

Lamarin ya kuma jefa su a cikin halin wawa ni kayi, inda kuma hakan ya shafi tattalin arzikin kasar.

 

Exit mobile version