Umar A Hunkuyi" />

Korona: Dalibin Nijeriya Ya Mutu Makonni Kafin Ya Sauke Karatunsa

Makwanni kadan da su ka rage wani dalibi dan Nijeriya da ke karatu a Jami’ar Western Michigan Unibersity ta kasar Amurka ya kammala karatunsa mai suna Bassey Offiong, sai ga shi ya mace a sakamakon kamuwa da cutar nan ta Koronabairus.

Dalibin mai shekaru 25 da haihuwa a Duniya yana karantar kimiyyar hada sinadarai ne a Jami’ar ta Michigan.

Wata ta kusa da mamacin ta shaida wa wakilinmu cewa, a ranar Juma’a ce a ka yi wa mamacin gwajin ko ya kamu da cutar, wanda kuma gwajin ya tabbatar da kamuwarsa da cutar ta Koronabairus.

‘Yar uwan nashi mai suna Rosalyn Afiong, ta kara da cewa, dalibin ya rasu ne a ranar Lahadi, inda kuma ta kwatanta mamacin da cewa haziki ne mai baiwar kwakwalwa.

A cewar ‘yar uwar na shi, sau da yawa ana ta son a yi wa Offiong gwajin ko ya kamu da cutar amma sai ya ki amincewa a yi masa gwajin duk kuwa da alamomin kamuwa da cutar da suka bayyana a gare shi.

Ta ce mamacin ya yi fama da wahalar yin numfashi, ramewa da kuma zazzabi mai tsanani kafin mutuwar nashi.

 

Exit mobile version