Bisa yadda duniyar sufurin jiragen sama ke fuskantar matsalolin sake dawowar cutar Korona, hukumar kula da fiyayen jiragen sama ta Nijeriya (FAAN), ta dauki matakin yin gwaji a fadin filayen da ke kasar nan domin kare lafiyar matafiya.
Tun daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke garin Abuja da filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas da filin jirgin sama na Fatakwal da filin jirgin sama na Mallam Aminu da ke Jihar Kano da sauran filayen jiragen sama da ke gudanar da jigila, an dauki wannan mataki na tsare matafiya daga kamuwa da cutar Korona.
An bayan da jami’ar hudda da jama’a na hukumar FAAN, Misis Henrietta Yakubu ta rattaba hannu, ta bayyana cewa an samu sabon yarjejeniyar gudanar wa a dukkan filayen jiragen sama, wadanda suka hada da tsarin wajen ijiye motoci domin kaucewa cinkoson ababan hawa a filayen jiragen saman. Ta kara da cewa, mahukuntan sun dauki wannan matakai ne domin kare rayukan fasinjoji.
Yakubu ta ce, “an dauki wannan mataki ne domin kare dukkan wadanda ke zuwa filayen jiragen sama da kuma saukaka zirga-zirga.
“Ina shawartan dukkan matafiya da masu amfani da filayen jiragen sama da su bayar da hadin kai ga wannan mataki da aka dauka domin a gudu tare a tsira tare,” in ji ta.