Connect with us

MANYAN LABARAI

Korona: FCTA Ta Hada Kai Da NOA Kan Sabbin Hanyoyin Wayar Da Kai

Published

on

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana shirinta na hada kai da hukumar wayar da kai ta kasa (NOA), domin kaddamar da wasu sabbin hanyoyin wayar da kai a kan yaki da annobar Korona.

Babban jami’in hulda da manema labarai na hukumar babban birnin tarayyan, Mista Anthony Ogunleye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, y ace Ministan babban birnin tarayyan, Musa Bello, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da babban daraktan hukumar wayar da kan ta kasa, Dakta Garba Abari.

Ogunleye ya ce taron wanda shugaban kwamitin kwararru masu bayar da shawara a kan annobar ta Korona, a hukumar babban birnin tarayyan, Dakta Aliyu Modibbo, ya halarce shi.

Ministan ya bayyana cewa hadakar an yi ta ne da nufin karfafa dubarun wayar da kan al’ummomin babban birnin domin kare rayuka da dukiyoyi, wanda annobar ta Korona ke ta faman halakawa.

Sai dai ya yi jimamin yanda da yawan mazauna babban birnin tarayyan suke ci gaba da musanta aukuwar annobar da kuma hadurran da suke tattare da ita, wanda hakan ya sanya sam ba sa daukan matakan da suka dace domin dakile yaduwarta.

“Hakan ne ya tilasta samar da wasu sabbin dubarun wayar da kan ta yanda sakon zai kai ko’ina,” in ji Ministan.

Ya yi nuni da cewa hadakar babban birnin tarayyan da kuma kungiyoyi wacce kwararren mai bayar da shwara na hukumar babban birnin tarayyan yake tsarawa, hakan ya kai babban birnin tarayyan ga samun nasarori masu yawa a kan yaki da annobar ta Korona, ta hanyar samar da isassun gadaje da kayan magani gami da ma’aikatan lafiya.

Ya ce ya amince a wajen taron da cewa za a kafa kwamitin da zai tsara yanda za a tafiyar da sabbin tsare-tsaren domin shiga mataki na gaba a kan yakin da ake yi da annobar ta Korona.

Bello ya bayyana cewa, kwamitin wanda Abari da Modibbo za su shugabance shi ya kunshi wakilai daga hukumar babban birnin tarayyan da kuma hukumar wayar da kan ta kasa.

Da yake na shi jawabin, Abari cewa ya yi taron na su ya kara karfafa dangantakar da ke tsakanin hukumar ta su da kuma hukumar babban birnin tarayyan gami ma da sauran kungiyoyi masu zaman kansu a kan yakin da ake yi da annobar ta Korona.

Ya ce sabuwar hanyar wayar da kan wacce aka yi mata lakabi da, ‘CObID-19 New Normal FCT Response,’ ba a kafata ba fiye da abin da ya fi kokarin wayar da kai, amma za ta fara ne da gyara halaye ga mazauna babban birnin tarayyan.

“Wannan sabuwar hanyar an kafa ta ne domin gyara halayen mazauna babban birnin domin su kula da lafiyarsu.

“Hukumar wayar da kan tana da kwarewa wajen isar da sabon sakon a kan tituna, Unguwanni, wuraren ibada da kuma masarautu, hakanan za kuma ta wayar da kai a kan matsalar da ke akwai wajen daukar cutar a kana bin da ya shafi daidaikun mutane,” in ji Abari.

A cewar babban daraktan hukumar wayar da kan ta kasa, hukumar na shi tana da kwarewa kuma tana da duk abin bukata na kwararrun ma’aikata da ingantattun kayan aiki wajen yada sabon sakon.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: