Hukumar kwallon kafa ta Duniya, wato Fifa, ta sanar da dage gasanin cin kofin duniya na ’yan kasa da shekaru 17 da 20 da ya kamata a yi a cikin wannan shekara ta 2020 zuwa shekara ta 2023 sakamakon yadda cutar annobar Korona ta sake dawowa a karo na biyu.
Hukumar ta Fifa a wannan sanarwa ta na mai bayyana cewa annobar coronavirus ba za ta bayar da dama a gudanar da wadannan wasani da aka saba ganin ana tara jama’a a lokutan buga wasannin ba hakan yasa ta nemi shawarwarin masu ruwa da tsaki da kasashen da za su halarci wasannin kuma bayan haka take ganin ya kamata a dage wasannin zuwa shekara ta 2023.
Shugaban hukumar ta Fifa, Gianni Infantino, ya shaidawa manema labarai cewa cutar Korona c eta sanya dole ba zasu ya shirya wasannin ba saboda lafiyar ‘yan wasa da shugabanni itace a gaba da komai a tsarin Fifa.
“Abin takaici ne cewa ba zamu iya gudanar da wadannan wasanni ba a wannan shekarar sai dai ya zama dole mu dage wasannin saboda halin da duniya take ciki na annoba kuma muma a matsayin mu na shugabanni dole mu kare rayukan wadanda muke shugabanta” in ji shugaban