Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Ganduje Ya Karbi Bakuncin ‘Yan Majalisar Wakilai

Published

on

Tawagar ‘Yan Majalisar Wakilai na Tarayya, sun ziyarci Gwamnan Jihar Kano Dakata Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin gudanar da taron mane ma Labarai kan cutar Korona da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, ranar Talatar da ta gabata, kamar yadda Darktan Yada Labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.
Tawagar karkashin jagorancin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, sun hada da Wakilan Majalisar daga Jihar Kano da kuma kwararru akan harkokin lafiya.
Da ya ke gabatar da jawabinsa, Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa dalilin wannan ziyara shi ne, domin jajantawa tare da nuna goyon baya ga Gwamnatin Jihar Kano, bisa kokarin da ta ke yi a kan yaki da annobar Korona a fadin jihar baki-daya.
“A madadin Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma daukacin ‘Yan Majalisar Wakilai, muna gabatar da sakon jaje tare da nuna damuwarmu kan halin da ake ciki a Jihar Kano, kamar yadda ya shaida wa Gwamnan.”
Haka zalika, Alhassan Ado Doguwa ya jagoranci gabatar da kuduri a lokacin zaman Majalisar da ya gudana ranar Talata, akan halin da Jihar Kano ke ciki.
“Matsayar da muka dauka shi ne, neman Gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar kwakkwaran mataki, domin dakile wannan annoba da sauran abubuwan da ke faruwa a Jihar ta Kano, kasanewar Kano na da muhimmacin gaske ga Gwamnatin Tarayya, musamman matsayinta na Cibiyar ciniki a yankin Arewa baki-daya, duk abinda ya shafi Kano babu shakka ya shafi  sauran bangaren kasa baki-daya,” in ji shi.
Shugaban Masu Rinjayen, daga nan sai ya gabatar da kwafin takardar kudurin da ya gabatar wanda ya samu amincewar mafi yawancin Wakilan, inda ya bukaci a tallafawa Gwamnan Jihar Kano kan wannan al’amari.
Da ya ke gabatar da nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana farin cikinsa ga Wakilan Majalisar daga Jihar Kano bisa kokarinsu na neman tallafi daga Gwamnatin Tarayya, domin dakile wannan annoba ta Koranabairos a Jihar Kano.
“Ina kara jinjina muku tare da Abokan aikinku na Majalisar Dattijai, bisa nuna damuwa gare mu a wannan matsanancin lokaci, ko shakka babu kun kasance ingantattun wakilan al’ummar da kuke wakilta”, a cewar ta Ganduje.
Haka nan kuma, Gwamnan ya gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa aiko da tawaga da ya yi, daga Kwamitin nan na kar-ta-kwana akan wannan cuta ta Korona na Gwamnatin Tarayya, domin taimaka wa kokarin Gwamnatin Jihar Kano wajen dakile yaduwar wannan annoba.
A jawabinsa tunda farko, Jami’in tsare-tsaren matakan gaggawa na Jihar Kano, Dakta Tijjani Hussaini ya bayyana cewa, a kokarin da suke yi na magance cutar a Jihar Kano, sun samu damar bibiyar wadanda suka yi mu’amala da wadanda ake zaton sun kamu da wannan cuta su kimanin 267 daga cikin 25, da aka hangi alamun cutar a tare da su, yayin da uku daga cikinsu kuma aka sallame su.
Da ya ke yin tsokaci akan matakan tsaro, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano Alhaji Ahmad Habu Sani cewa ya yi, matakan da suke dauka domin tabbatar da ganin tsarin zaman gida ya gudana yadda ya kamata, wanda ya hada da wayar da kan al’umma, rufe dukkanin  iyakoki da samar da wurare bincike, kame dukkannin wadanda suka yi kunnen kashi, takaita zirga-zirga da kuma samar da hadin kan dukkanin Hukumomin tsaro a Jihar Kano.
Har ila yau, a cikin wadanda suka halarci ganawar akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna, Kwamishinoni da sauran Shuwagabannin sassan Gwamnati daba-daban na Jihar Kano.
Advertisement

labarai