Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Gombe Za Ta Samar Da Takunkumi Miliyan Daya Kyauta

Published

on

Gwamnatin jihar Gombe za ta samar da abin rufe baki da hanci (Face Masks) sama da miliyan daya gami da rabar wa jama’a kyauta a fadin jihar, musamman marasa hali a cikin al’umma domin ci gaba da kokarin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin yaki da cutar Korona a jihar, Farfesa Idris Muhammad a jiya lokacin da ke amsar tallafin kayyakin kariya da ofishin NYSC a jihar Gombe suka hada da kansu gami da mika wa gwamnatin jihar domin ci gaba da yaki da cutar.

Farfesa Idris ya ce, shirye-shiryen daukan matakin da kowa zai ke sanya abin rufe hanci da baki na kan hanya, sai dai ya ce kafin su kai ga fitar da wannan matakin kwamitin zai yi kokarin tabbatar da kowa ya samu abin rufe hanci da bakin kafin a dauki matakin tilasta wa kowa amfani da shi.

Shugaban kwamitin yaki da cutar, ya kuma kara da cewa tunin aka kama aikin samar da abin rufe hanci da bakin wanda ana kan aiki tukuru, ya kuma shaida cewar nan da ‘yan kwanaki za su wadatu tare da rabar wa jama’a.

Daga bisani ya gode wa NYSC a bisa tallafa wa gwamnatin jihar da suka yi a irin wannan lokaci da ya kasance mawuyaci, ya kuma kara da cewa tabbas tallafin zai taimaka wa gwamnatin wajen cimma nasarar kai wa kowani gida abin rufe hanci da baki tare da sinadarin wanke hannu.

Ko’odinetan NYSC a jihar Gombe, Florence Yaakugh a lokacin da take gabatar da kayyakin, ta shaida cewar hukumar ta mori ababe da dama daga wajen gwamnatin don haka suka ga dacewar su kawo nasu tallafin a irin wannan lokacin da duniya ke kan yaki da annobar Korona.

Ta kara da cewa, NYSC ta yi amfani da halin da ake ciki ta fuskacin hada kayyakin da hannunta domin taimaka wa kokarin gwamnatin jihar na yaki da cutar.

Wakilinmu ya shaido cewar kayyakin da NYSC suka taimaka wa gwamnatin Gomben sun ha dada sinadarin wanke hannu guda 120, fakej-fakej na abin rufe hanci da baki guda 160, sabulun wanke hannu guda 60.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: