Khalid Idris Doya" />

Korona: Gwamna Bala Ya kaddamar Da dakin Gwaje-gwajen Cututtuka A Bauchi

Jiya ne Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bude cibiyar gwaje-gwajen cutuka a Bauchi domin tabbatar da shawo kan cutuka masu yaduwa tare da dakilesu musamman cutar nan da ta addabi duniya ta Korona.

Da ya ke jawabi a kajen kaddamar da fara amfani da cibiyar da ke asibitin kwararru na Bauchi, Gwamna Bala ya shaida cewar samar da cibiyar zai taimaka matuka wajen inganta kiwon lafiyan jama’a a jihar da ma kasa baki daya, ya na mai cewa cibiyar za ta ke gwajin cutukar da suka shafi Korona, zazzabin lassa, shawara, da sauran cutuka da suke haduwa a tsakanin jama’a.

Ya kuma shaida cewar samar da cibiyar gwajin cutukan hadin guiwa ne a tsakanin hukumar bunkasa shiyyar arewa maso gabas NEDC da kuma cibiyar dakile cutuka ta kasa NCDC, inda ita kuma gwamnatin jihar ta samar da kudaden ginin muhallin da aka kafa cibiyar a ciki gami da sauran kayan da suka dace.

Bala Muhammad ya sha alwashin gwamnatinsa za ta ci gaba da bada nata gudunmawar wajen kyautata sashin lafiya domin jama’an jihar suke kasancewa masu cikakken lafiya da koshinta a kowani lokaci.

Gwamna Muhammad ya kuma sanar da cewar za su ci gaba da zuba jari wajen gyarawa da samar da cibiyoyin lafiya tare da tulin kayayyakin da suka shafi na inganta kiwon lafiya.

A cewarsa za su ci gaba da yin hadaka da kungiyoyin da suka dace domin kyautata kawon lafiyan jama’an jihar.

A cewarshi samar da cibiyar wata dabarace ta tabbatar da dakile bazuwar cutar Korona a tsakanin jama’a.

A jawabinsa Manajan gudanarwa na NEDC, Alhaji Mohammed Alkali ya jaddada aniyar hukumar na taimaka wa jihohin da suke shiyyar arewa maso gabas ta fuskacin yaki da korona da sauran sassan da za su kai ga kyautata shiyyar.

A cewarsa da hadin guiwar gwamnatin jiha da hadin guiwar masu ruwa da tsaki hukumar za ta ci gaba da kyautata shiyyar arewa maso gabas musamman a kokarinsu na yaki da cutar Korona.

Exit mobile version