Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Gwamnati Za Ta Tsaurara Dokar Takunkumi

Published

on

A ranar Litinin ce gwamnatin tarayya ta shelanta cewa za ta kara tsanantawa wajen tilasta yin amfani da takunkumin nan na rufe baki da hanci a cikin jama’a, musamman wuraren ayyukan gwamnati da wuraren gudanar da harkokin kasuwanci.

Duk wanda aka kama ba ya sanye da takunkumin za a hana ma shi shiga duk wani wajen da jama’a su ke, ba kuma za a karbe shi a duk wani abin da ya je nema ba a wajen gwamnati; gwamnatocin Jihohi ne ke da alhakin tabbatar da ana bin dokar sau da kafa, babban jami’in tsara shirin kwamitin yaki da annobar ta korona, Dakta Sani Aliyu, ne ya shaida hakan.

Da ya ke magana a lokacin ganawa da manema labarai kamar yanda kwamitin ya saba a kullum a Abuja, ya ce kashi na biyu na shirin saukaka dokar hana zirga-zirgan shi ma za a tsawaita shi ne na tsawon wasu makwanni hudun daga yau Laraba.

Ya ce: “Yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci yana nan a matsayin tilas za kuma a kara tsananta shi a dukkanin matakai, da suka hada har da gwamnatocin Jihohi.

“Samun shiga duk wani waje na gwamnati da wuraren harkokin kasuwanci ba zai yiwu ba ga kowa face wanda ya ke sanye da takunkumin.

“Dokar hana zirga-zirga kuma wacce ke fara aiki daga karfe 10 na daren kowace rana zuwa karfe 4 na asubahi tana nan daram a duk sassan kasar nan.

Aliyu ya ce ba wani canji a kan ka’idojin yanda ake shiga kasuwanni, otal-otal, wuraren cin abinci da wuraren motsa jiki har da wuraren daurin aure da jana’iza.

Kananan hukumomi su ne za su kula tare da tabbatar da ana yin aiki da dokokin, ya kara da cewa, bankuna kuma za su ci gaba da yin ayyukansu a lokutan da aka iyakance masu.

Aliyu ya ce: “Ga kamfanoni da masana’antu, za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a kayyadaddun lokutan da aka kayyade masu, in ban da ofisoshin gwamnati da su ke da na su lokutan aikin na daban. Dukkanin ofisoshin tilas ne su rika yin aiki kashi 75 na lokutan aikin na su kadai.

“Ga masu sana’o’in kansu kamar makanikai, kafintoci, magina, masu sana’ar gyaran gashi da sauran su, wadanda su ke da shaguna da wuraren aikinsu an amince masu da su ci gaba da gudanar da ayyukan na su kamar yanda suka saba.

“Tilas ne wuraren cin abinci su ci gaba da kasancewa a kulle ga masu siyan abinci su kuma ci a wajen, tilas ne kuma wuraren su ci gaba da kasncewa a cikin tsafta, face wuraren cin abinci da su ke aiki a otel.

“Wuraren motsa jiki, gidajen Sinima, wuraren taruka da klub-klub din dare duk za su ci gaba da kasancewa a kulle wanda kuma za a tabbatar da hakan na yin aiki.

“Ga wuraren jana’iza da daurin aure, ba wani canji a kan yanda a ka saba, amma duk wuraren tilas ne ya kasance mahalartansa ba su wuce adadin mutane 20 ba, da suka hada har da iyalin wajen.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: