Connect with us

LABARAI

Korona: Gwamnatin Bauchi Ta Zaftare Naira Biliyan 39 Daga Kasafinta

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da zaftare kasafin kudi na 2020 daga naira biliyan N167b zuwa N128b tare da rage wasu aiyukan da basu da muhimmanci hadi da kara yawan kason sashin lafiya domin a samu zarafin dakile annobar Korona da sauran kalubalen da suke sashin lafiya.

Adadin kudin da  jihar ta yanke daga cikin kasafin kudin ya kai naira biliyan 39 da aka yi dogon nazarin matakin da ake ciki da yanayin da ake fuskanta musamman na yaki da cutar Korona tare da kalubalen da tattalin arzikin jihar ya samu kansa sakamakon matsalar ta Korona.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Dakta Aminu Hassan Gamawa shine ya shaida wa manema labaru hakan a karshen ganawar mambobin majalisar zartaswa ta jihar (SEC) a ranar Laraba da ya gudana a gidan gwamnatin jihar, yana mai shaida cewar daukan matakin zaftare kasafin ya zama dole ne lura da halin da annobar Korona ta jefa tattalin arzikin jihar kasa da ma duniya baki daya.
Yana mai bayanin cewa a sakamakon fadin farashin dayen Mai a kasuwannin duniya don haka ne suka lalubo hanyoyin da za su samu zarafin gudanar da mulki tare da aiwatar wa al’ummar jihar kyawawan aiyuka a irin yanayin da ake ciki daidai da tattalin arzikin da jihar ke harsashen samu.
Ya ce, sabon harsashen kasafin da suka fitar za su aike da shi gaban majalisar dokokin jihar domin amincewa gabanin gwamnan jihar Bala Muhammad ya sanya hannu a kai don zamar da kasafin cikin doka tare da bin dukkanin matakan da shari’a ta gindaya.
A cewar kwamishinan a kan wannan matakin jihar za ta bada aiyukan da za a aiwatar ne kawai ba tare da biye wa aiyukan da ba su da wasu muhimmaci ko wadanda za a watsar da su ba, inda ya nanata cewar gwamnatin za ta aiwatar da muhimman aiyukan da suka dace ne kawai kuma muhimmai daga ciki.
Aminu Gamawa yana mai cewa a bisa sake aiki kan kasafin an samu zarafin shigar da karin muhimman abubuwan da suka dace musamman a bangaren lafiya domin dacewa da halin da ake ciki da kuma yanayin da jihar da al’ummar jihar za su fi mora.
Dangane da batun albashi mafi karanci kuwa, Kwamishinan ya shaida cewar gwamnati tana kan nazartar lamarin har zuwa lokacin da za ta kammala zartas da matakin dauka dangane da batun sai dai ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar ba za ta taba sakewa ta yi wasa da albashin ma’aikata da sauran hakkokin ma’aikatan jihar.
Daga nan sai ya nemi hadin kan jama’an jihar da su taimaka wajen mara wa gwamnati mai ci baya domin ta samu nasarar cika alkawuran da ta dauka musu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: