Khalid Idris Doya" />

Korona: Gwamnatin Bauchi Za Ta Yi Kwaskwarima Ga Kasafin 2020

Annobar cutar Koronabairus da ke ci gaba da yi wa tattalin arzikin kasashe tarnaki, ya tilasta wa gwamnatin jihar Bauchi daukar matakin sake waiwayar kasafin kudin shekarar 2020 domin sake nazari tare da sauya abubuwan da ake hasashen aiwatarwa lura da matsalar da tattalin arzikin jihar ya fada sakamakon annobar Korona.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Dakta Aminu Hassan Gamawa shine ya shaida hakan bayan tattaunawar majalisar zartaswar jihar ta yi kan barazanr korona a jiya, inda ya ce kwaskwarima da za a yi wa kasafin za a shigar da muhimman abubuwa ne kawai tare da cire abubuwan da basu da muhimmanci lura da halin da tattakin arzikin jihar ya samu kansa a ciki.
“A nawa ma’aikatan mun bada shawara dangane da yanda annobar Korona ta ke tasiri kan tattalin arzikin jihar Bauchi. Kamar yadda kowa ya sani a sakamakon annobar farashin danyen Man Fetur ya fadi a kasuwannin duniya. Sannan kudaden da muke samu na shiga na cikin gida da wanda ake samu daga Abuja dukka sun ragu.
“Abin da muka yanke shine jihar Bauchi ya dace ta dauki wasu matakan da za a tafiyar da harkokin gwamnati ba tare da an samu manyan matsaloli ba.
“Gwamna ya umurci a je a sake duba kasafin kudi na shekarar 2020 domin yi masa kwaskwarima domin ya zama abubuwan da aka sanya a ciki abubuwa ne da ana da kudaden da za a iya aiwatar da su kuma wadanda suka dace. Za mu tabbatar abubuwan da suka shafi albashi da walwalar jama’a an kula da su. Za mu kuma tabbatar ba mu sanya abubuwan da babu kudin aiwatar da su ba. tun a baya daman mun yi wannan kwafin kudin da harkar gudanar da mulki za a yi sune bisa gaskiya da adalci.”
Ya ce a yanzu haka da ake ciki gwamnan jihar ya kafa kwamiti da zai duba hanyoyin da cutar Korona ya shafi tattalin arziki tare da duba hanyoyin fita daga wannan matsalar na tarnakin da tattalin arziki ke fuskanta.
Ya ce, kwamitin ya bada shawarar kira ga jama’a da kowa ya koma gona, ya ce akwai kasar noma mai kyau a jihar domin haka jama’a su dukufa su koma noma domin a samu abinci da za ci, “Sannan gwamnati za ta takaita yawan kashe kudade da a ke yi ta yadda za kashe kudade ne kawai a kan abubuwan da suke da gayar muhimmanci,” a cewar kwamishinan.

Exit mobile version