Korona: Gwamnatin Filato Ta Maido Da Almajirai 190 Bauchi

Biyo bayan haramta Almajiranci da gwamnonin arewacin Nijeriya suka yi, gwamnatin jihar Filato ta maido wa gwamnatin Bauchi almajirai 190 tare da malaminsu da suke zaman almajiranci a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Gwamnonin arewacin Nijeriya su 19 sun dauki matsayar haramta almajiranci tare da hana barace-barace ne a kokarinsu na kare kai daga yaduwar cutar Korona.

Gwamnatin Bauchi ta amshi Almajiran ne a makarantar sakandarin Janar Hassan Usman Katsina Unity College, Yelwa, inda mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela ya amshesu, ya kuma ce jihar tana tsumayar sauran jihohin da akwai almajiran jihar a jihohinsu da su dawo wa Bauchi da ‘ya’yanta.

Baba Tela wanda shine shugaban kwamitin yaki da Korona a jihar, ya kuma kara da cewa, su ma jihar Bauchi za su kwashi almajirai da malamansu da suke jihar tare da maidasu jihohinsu na asali daga yau Litinin.

Tela ya ce daukar matakin na daga cikin matsayar da gwamnonin arewa suka dauka na tabbatar da dakile yaduwar korona lura da barazanar hanzarin yada cutar da almajiran ka iya yi idan aka yi sake.

Wakilinmu ya nakalto cewar gwamnatin ta amshi almajiran wadanda mafi yawansu yara ne tare da ajiyesu a makarantar na wucin gadi domin duba lafiyarsu gami da duba ko suna dauke da cutar korona ko a’a.

Daga bisani kuma za a killace su na tsawon kwanaki 14 a sansanin NYSC da ke Bauchi domin kula da lafiyarsu, daga bisani za a kaisu kauyukansu na asali bayan kwanaki 14 a killace.

Exit mobile version