Korona: Gwamnatin Kaduna Ta Fitar Da Sabbin Dokoki

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai, ya amince bayan ya duba rahoto kan yadda dokar garkame mutane ya gudana a Kaduna, sannan ya bayyana cewa daga wannan mako sau daya za a rika fita zuwa kasuwanni da dan walwala, ba kamar yadda dokar ta ke a baya ba, wanda kunshi ranar talata da labara ba, yanzu dokar ta kebe ranar labara ne kawai aka baiwa jama’a damar fita.

Dokar ta bayyana cewa, daga yanzu ranar Laraba ne kawai za arika fita, har sai an samu sahihan bayanai na an iya kakkabe wannan cuta baki daya.

Sannan kuma duk wanda zai fita daga gidan sa daga yanzu sai ya saka takunkumin fuska dole kuma ayi nesa-nesa da juna a kasuwanni da zaman cikin mota.

Gwamnati za ta wadata gajiyayyu, da wadanda basu da halin siyan takunkumin fuska. Bayan haka an yi kira ga mutane su garzaya ga tailoli domin su dinka musu takunkumin da za su iya wanke wa idan ya yi datti.

Dokar ta kara da bayyana cewa, dole a saka takunkumin fuska a fadin jihar baki daya, domin kare kai daga kamuwa da cutar, sannan dole kowa ya zauna a gida.

Ba a yarda a bude ofisoshi ba, Kasuwanni, wuraren shakatawa, shaguna, masallatai da coci-coci, wato wuraren bauta.

Dokar ta bayyana cewa, wadanda aka yarjawa su ci gaba da zirga-zirga su ne, ma’aikatan kiwon lafiya, ma’aikatan Kashe gobara, ma’aikatan albarkatun ruwa da wutan lantarki, ‘yan jaridu, sannan kuma da jami’an tsaro, sannan da tankoki dake jigilar daukar man fetur. Sannan wuraren saida abinci da kayan asibiti za a samar musu da tsaro.

Dokar ta bayyana cewa, Makarantu, wuraren ibada, wuraren shakatawa, filayen motsa jiki, gidajen giya, duk zasu ci gaba da zama a kulle.

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta hori mutane su ci gaba da zaman gida, sannan su rika nesa-nesa da juna kuma a gujewa shiga taro ko cunkoso, a saka takunkumin fuska sannan a rika wanke hannu da ruwa da sabulu.D

Gwamnati ta bayyana cewa, duk matafiyin da ya shigo Kaduna da gangar, za a killace shi na tsawon kwanaki goma 14, ko kuma ya koma inda ya fito, sannan kada ya dauka za a killace shi don nishadi ne.

Dokar ta ce, duk motar da aka kama shikenan mai ita zai rasa ta har abada domin zai koma mallakin gwamnati, sannan duk kamfanin dake da mallakin wannan mota zai fuskanci hukunci, domin za a kai shi kotu sannan za a kwace lasisin yin aiki a Jihar Kaduna. Shi ma direban wannan mota sai ya biya tara ko a daure shi.

Haka kuma, an dakatar da ayyukan Keke Napep, Acaba, Tasi da sauran su, duk wanda aka kama za a kwace abin hawan na dindindin, zai zama na gwamnati.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa ta kirkiro Kotun tafi da gidan ka da za ta rike yanke hukunci nan take. Sannan nan take za ka biya tara, in dauri ne ma duk a nan za a yanke maka hukunci sannan kuma, idan kwace abin hawanne ma duk a nan ne za a kwace.

Haka kuma motocin daukar mai, abinci, taki da kayan gona, kayan asibiti duk ban da su, sai dai suma din kada su wuce mutum uku a ciki.

Duk wanda ya yi wa gwamnati sojan gona, wajen yi kamar shima mai jigilar kayan abinci ne, za a tuhume shi sannan a kwace masa motarsa ta zama na gwamnati.

Bayan haka, gwamnati ta ce ta umurci duka Shugabannin kananan hukumomin Jihar kaduna, su tabbatar wannan doka ya tabbata a kananan hukumomin su.

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta umarci duka manyan ma’aikatan ta, da suka hada da kwamishinoni, Manyan Sakatarori, masu ba gwamna Shawara, shugabannin ma’aikatu, su ba da gudunmawar naira 500,000 a wannan watan Afrilu. Sannan za su rika bada rabin Albashin su duk wata har sai an bude gari.

Ma’aikatan gwamnati dake karbar albashin naira 67,000 duk wata za su rika bada kashi 25% na albasin su duk wata har sai an bude gari. Babu wani ma’aikaci da zai rasa kasa da naira 50,000, da zai rika maneji har zuwa a bude gari.B

Bayan haka, Gwamnatin Jihar zata yaba wa duk wanda ya taimakawa jihar da kudi, kayan abinci, magani da sauran su. Sannan kuma za a bayyana irin taimakon da ya bada baya ga takardar yabo da za a bashi. Duk a cewar Gwamnatin Jihar Kaduna.

Exit mobile version