Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i, ta kara daukar kwakkwaran mataki na dakile bazuwar cutar korona, bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da Gidajen rawa.
A wani sako da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fitar ya sanar da cewa, daga ranar Litinin 21 ga Disamba, 2020, ma’aikatan Jihar kaduna ‘yan kasa da mataki na 14 su ci gaba da zama a gida da gudanar da ayyukan su daga gida har sai abin da hali ya yi.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da aka tabbatar da samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a ‘yan kwanakin nan.
A makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa ta rufe makarantu kafin daga bisani ta sanar da cewa ta bayar da umarni rufe wuraren taron bikin da Gidajen rawar disko.
A ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da umarnin rufe dukkan wasu wuraren taron biki, Gidajen rawar disko, da cibiyoyin motsa jiki, a wani yunkuri na dakile yaduwar kwayar cutar korona a karo na biyu.
Kazalika, Gwamnatin Jihar kaduna ta takaita harkokin wuraren sayar da abinci; babu zama a ci, sai dai a kunshewa mutum abincinsa ya tafi da shi, duka dai domin ragewa cutar karsashi. A cewar Gwamnatin Jihar Kaduna.