Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli na Jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya jaddada aniyar Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na yin duk mai yiwuwa, domin kare lafiyar al’ummar Kano daga kamuwa da wannan annoba ta Koronabairos, kamar yadda Jami’in Yada Labaran Ma’aikatar Muhalli na Jihar Kano, Abbas Habeeb Abbas ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.
Kwamishinan ya bayyana haka ne, a lokacin da ya jagorancin tawagar Ma’aikatar zuwa Unguwar Rijiyar Zaki, domin duba wuraren da ake zargi wani wanda ya ke dauke da wannan cuta ta Koronabairos ya ziyarta.
Ya ce, yana daga cikin tsare-tsaren wannan Gwamnati, wanda ake aiwatarwa ciki har da hana zirga-zirga baki-daya, kamar dai yadda ake gani a halin yanzu. Babbar hikimar daukar wannan mataki shi ne, domin dakile yaduwar wannan cuta wanda hakan zai kara taimakawa wajen zakulo wadanda suka yi mu’amala da kuma wuraren da mai dauke da wannan cuta ya ziyarta.
Ya kara da cewa, wannan na cikin cigaban da ayyukan da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar a ranar 28 ga watan da ya gabata, musamman na gudanar da feshin magani a wuraren taruwar al’umma, wadanda suka hada da Kasuwanni, Masallatai, Coci-Coci da kuma tashoshi mota da sauran makamantansu.
Kamar yadda Gwamna ya bayar da umarni, an dorawa wannan Hukumar alhakin gudanar da feshin magani a dukkanin wuraren da ake zargi wani mai dauke da cutar ya ziyarta.
“A yau ne muka samu kira daga wasu masu kishin al’umma, inda suka ba mu labarin cewa wani wanda ake zargi da kamuwa da wannan cuta, ya ziyarci Masallatai guda uku, inda muka gudanar da feshin magani domin kawar da duk wata kwayar cuta.
Har ila yau, Dakta Getso ya nuna farin cikinsa bisa yadda jama’a ke bayar da bayanan abubuwan da ke faruwa a yankunansu, haka kuma ya godewa jama’ar Kano bisa hadin kan da suka nuna wajen bin dokar zama a gida wadda Gwamnatin Kano ta zartar, babu shakka hakan ke taimakawa wajen hana yaduwar wannan cuta ta Korona.
A karshe, Kwamishinan ya bukaci al’ummar Jihar Kano da su cigaba da nisantar cinkuso tare da wanke hannu da sabulu ko kuma yin amfani da sinadarin tsaftace hannu. Sannan kuma, ya bukaci jama’a su gaggauta sanar da Hukumomi akan duk wata alama da suka gani wadda ta shafi wannan cuta.