Korona: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Jihar Gombe Buhun Shinkafa 1, 800

Ma’aikatar tallafawa da jinkai ta gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Gombe tallafin buhun shinkafa 1, 800 a wani mataki na tallafawa al’umma domin saukaka musu dangane da cutar Korona.

Da yake mika kayayyakin a Gombe a ranar Juma’a, Malam Grema Alhaji, Daraktan sashen tallafawa al’umma na ma’aikatar, ya ce sun tallafawa gwamnatin jihar a wani mataki na saukakawa al’umma kan yaki da cutar Korona da ake yi a duniya.

Tallafin rahotanni sun tabbatar da cewa tallafin za a bai wa zawarawa ne, da kuma nakasassu da marasa galihu.

Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Gombe, mataimakin gwamnan jihar, Manessah ya mika godiyarsu ga gwamnatin tarayyar, inda ya ce za su raba shinkafar ga wadanda aka bukaci a ba su.

 

Exit mobile version