Connect with us

LABARAI

Korona: Gwamnatin Tarayya Ta Fid Da Sharudda Shida Kafin Bude Makarantu

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta fidda sharuda guda shida nasake bude Makarantu.
Gwamnatin tarayya, ta bangaren Ma’aikatar Makarantu, tasanar da kulle makarantun primary, sekandari da jami’u na kasa a 19 March biyo bayan bullar cutar Korona.

Har ila yau dai, ma’aikatar tace zata sake bude makarantun muddun an cika sharudan da ta gindaya.

A yayin bayyana sharudan a Abuja, karamin minista akan fannin ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba yace, duk makarantu dole sai suna da:
1) Kayan wanke Hannu 2) Abun duba yanayin sanyi/zafin jiki 3) Abun feshin jiki a kofar shiga makarantun, Adakunan kwanan dalibai 4) duk fadin filin makaranta sai an kawar da duk abinda ka iya kawo cunkoso. 5) dole sai anyi kokari wajen tabbatar da tsafta. 6) kuma sai an tabbatar da nisantar juna.
Sannan Ministan ya gargadi masu Makarantu kan bude Makarantu batareda umarnin gwamnati ba.
“Bayan muna kan kokarin yin duk abinda ya dace muga mun kara kawo sauki kan kulle da ake ciki, muna rokon shuwagabannin Makarantu dasu dauki matakai nakariya tun yanzun bawai sai ankoma ba su fara neman kayan aikin da dokar gwamnati ta gindaya kan sake bude Makarantu.” Ya fada hakan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: