Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Wa Mabukata Rancen NIRSAL Rangwamen Kudin Rijista

Published

on

A kokarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun na ganin al’umma sun amfana da tallafin rance da Gwamnatin Tarayya za ta bayar, don ganin ‘yan kasuwar suncika gurbin asarar da su ka yi a lokacin annobar Korona, yanzu haka gwamnatin ta yi wa masu bukatar rancen rangwamen kudin rijistar horo, don ganin al’ummar sun amfana da shirin na NIRSAL.

Mai ba wa Gwamnan Jihar Zamfara Shawara a Hukumar Koyan Sana’a ta jihar, Hon. Amina Iliyasu Mafara, ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke tattaunawa da ‘yan jarida a hedikwatar ofishin da ke Gusau.

Hon Amina Iliyasu Mafara ta bayyana cewa, karkashin wannan Hukumar koyan Sana’a, yanzu haka tana raba Fam na samun rance da bankin kasa zaibada, dan farfado da harkar kasuwanci,sakamakon bollar annobar Korona ga kowa da kowa. kuma wannan tallafin rance ba zai samuba sai da sharadin mai bukatarsa yayi tireni kuma wannan tirenin sai anbiya kudin rijista, wasu jahohin kasar nan suna biyan kudin rijista tireni naira dubu goma sha takwas zuwa dubu ashirn,amma a wannan jihar tamu gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ya rage masu kudin rijista zuwa dubu goma sha biyu, dan ganin alummar jihar sun mafana da shirin inji Hon Amina.

Kuma wannan hukumar ta dukufa wajan wayar da kan jama’a, a koina cikin wannan jihar, akan wannan shirin tallafin da kuma yadda mutane zasu cika sharudan samun tallafin ba tare da matsala.

Hon Amina Mafara, ta kara da cewa, ‘ Wannan tallafin rance miliyoyin kudin masu kauri dan bunkasa harkar kasuwanci,akan haka te ke kira ga wadanda,zasu amfana da wannan shirin da su tafiyar da kudadan yadda ya dace. kuma su sani cewa ba kyauta bane rance ne, biya mutum zayi na addadin lokutan da aka dibar masa. dan haka sai ayi kafa kafa wajan tafiyar da Sana’ar da mutum zai yi.

A karshe Maiba gwaman Shawara tayi ma alummar jihar albishi na kokarin da gwamna Bello Matawallen Maradun keyi na farfado da Santocin koyan Sana’a takwas a cikin jihar dan ganin an koyawa matasa sana’ar hannu ta zamani dan dogaro da kan su.

A kan haka ne Hon Amina Mafara ta ke kira ga alummar jihar Zamfara da su ci gaba da baiwa gwamnatin goyan baya da addu’a dan ganin kodirinta ya cika na samar da tsaro da cigaban jihar baki daya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: