Connect with us

DUNIYAR MAKARANTU

Korona: Halin Da Dalibai Suka Shiga Sakamakon Rufe Makarantu (II)

Published

on

Ci gaba daga makon jiya

Sauda Idris:

Ni daliba ce a Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, ita kuma cewa ta yi, ni a ganin, awannan cuta ta Korona ta yi wa daliban Nijeriya illa da yawa zamu ga cewa wannan cuta ta mai da dalibai baya a wajen karatun da suke yi, kamar yadda aka tsara musu su,yi karatu, da kuma yadda za’a karantar da su, kuma in za mu duba za mu ga cewa karatun nan yaya yake kafin bullowar wannan cuta ballantan lokacin da wannan cuta ta bullo?.

In mun duba zamu ga cewa, wannan cutar ta yi wa dalibai illah da dama, na farko shi ne; za mu ga cewa dalibai sun zauna a gida da yawa wanda hakan illa ne akan karatunsu, na biyu shi ne ya mai da dalibai baya wajen yadda suke karatuttukansu, saboda wasu dalibai da ya kamata su gama a shekarar da ya kamata su gama, to ba a shekaran za su kamala ba dole sai sun kai wata shekarar.

In kun duba kamar wadanda suke karshen zango a karatun su sai wannan cutar ta bullo da kuma wadanda za su tafi bautar kasa duk ya bata musu al’amura. Kuma duba ga yadda dalibai suke zaune a gida za mu ga cewa wasu da dama sun mance inda aka dosa a wajan karatun da suka yi kafin kulle makarantun.

A ni karan kaina wannan kulle makarantun da aka yi ya dame ni, kuma na gaji da shi matuka, sannan kullen wannan makarantun ya ja wa dalibai zaman gida wanda ba su saba da shi ba, kuma wani abin haushi da takaici wanda wasu daliban Nijeriya suka shiga shi ne, akwai wadanda gab suke da fara jarabawa,  amman a dalilin wannan cutar ya sa an tsayar da rubuta jarabawar da za su yi, saboda tsawan lokacin nan da aka dauka ba karatu mafi yawancin daliban sun manta da abin da suka koya, domin gaskiya ba kowa bane zai iya tsayawa ya yi karatu da kanshi a gida, musamman ma a irin rayuwar da muka tsinci kan mu a ciki a yau, mutun yana zaune a gida ba tare da tallafi ba daga gwamnati ko kuma wasu al’umma, ta yaya har mutun zai zauna ya yi karatu, to in muka duba wannan zamu ga cewa ba karamin koma baya bane ga daliban Nijeriya.

Ana wata ga wata, ana shirye-shiryen bude makarantun kuma gashi babban al’amari yana shirin faruwa daman ya saba faruwa saboda wannan kungiya duk daliban da suke karkashin gwamnatin Nijeriya ‘yan ruwa ne”. Wato kungiyar jami’an daliban Najeriya cewa za su tafi yajin aiki, to dalibai ga Korona kuma ga ASUU wanne ya kamata ya zaunar da mu a gida?, Kasata Nijeriya wata kasa ce wacce ko ba Korona daman an saba barin mu a baya saboda a zahiri wannan kungiyar dalibai suke man aiki, amman a ba daili kansu suke wa aiki wataran ba kishin  dalibai suke yi ba kishin aljihunsu suke yi.

Wannan al’amarin kadai ya isa ya mai da daliban Nijeriya baya a wajan karatunsu, ba abin da za mu iya cewa sai dai muce Allah ya raba mu da zaman gida na gaira ba dalili, kuma Allah ya fidda mu daga “ruwa”. A nan zamu ga cewa ba wata maganar cigaba wajan kulle makarantun da aka yi illa kwarya-kwaryar koma baya da takaici da kuma ban haushi da daliban Nijeriya suka shiga da kuma yanayin tsara tsaran karatun su.

 

 

Salahuddeen Muhammad:

Sunana Salahuddeen Muhammad daga Jihar Kaduna a tarayyar Nijeriya, dalibi a jami’ar Al-Kalam da ke jihar Katsina, kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ita dai wannan cuta a yanzu haka ta kama sama da mutane 5.5 million a duniya, tare da kashe akalla mutum 400,000 kuma babban tashin hankalin shi ne har yanzu babu tabbacin takamaiman maganinta. Bullar wannan cuta ta haifar da matsaloli da dama ga kasashen duniya, musamman ta bangaren tattalin arziki, inda ta sabbaba karyewar farashin gangan danyen mai a kasuwar duniya, tare da hana jama’a walwala wanda hakan ta sa gwamnatoci a duk fadin duniya daukan tsauraran matakan hana yaduwarta.

A nan gida Nijeriya ma an samu bullar cutar a jikin mutane 12233, don haka gwamnatocin jahohi su ka bi sawun gwamnatin tarayya wajen kare yaduwar cutar ta hanyar garkame makarantu da kuma hana duk wa su taruka masu tara jama’a. To, ala ayyi-halin, idan za’a tuna a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne ASUU ta shiga yajin aiki inda ta kwashe watanni uku don nuna bacin ranta game da halin ko in kula da ta ce gwamnati na nuna wa ilimi a matakin jami’a. Duk da cewa Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce, gwamnati ta antaya wa ASUU Naira biliyan 25, amma shugaban ASUU ya ce, ba shi da masaniya game da wannan kudi, kuma ya ce babu wani Malamin Jami’a da ya samu wadannan kudade.

Kamata ya yi a ce gwamnati ta biya wannan kudi tun a watan Feburairun shekarar 2019 a matsayin wani kaso na bashin alawus-alawus da Malaman jami’a suke binta, amma sai yanzu take cewa wai ta biya, kuma babu wata jami’a da ta tabbatar da samun wannan kudi.

Don haka, su malaman jami’a ya kyautu su sake zama da yayan kungiyarsu don sanin matakin da ya kamata su dauka. Duba da wa su kasashe da su ka bude makarantu saboda an samu takaitar yaduwar cutar Korona, amma daga bisani su ka rufe saboda samun sabbin cases da aka yi, wanda hakan na iya shafar dalibai da su ke halartar darussa. Ya kamata a jinkirta bude makarantu saboda in an yi la’akari da kullum cases din yawaituwa yake yi a nan Nijeriya, kuma makaranta wuri ne da yake kawo cakuduwa na al’umma wanda yin hakan ka iya jefa daruruwan mutane cikin hatsari, sannan idan yiwuwar budewar ta taso ya kamata gwamnati ta bai wa hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) dama na su fitar da tsarin yadda za a bi na kaucewa balahirar wannan annoba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: