Dukkanin makarantun Firamare da na sakandari da suke jihar Kaduna har zuwa yanzu za su cigaba da kasance a kulle duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta bada damar bude makarantun a sassan kasar nan.
Kwalejin kimiyya da fasaha ta KadPoly da jami’ar karatu daga gida wadanda suka roki a ba su damar su sake bude makarantun domin baiwa dalibai damar zana jarabawa ne kawai aka amince musu sake bude makarantun biyu.
Babban sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta jihar, Misis Phoebe Sukai Yayi, ta shaida hakan cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi.
Ta ce: “Mun sani gwamnatin tarayya ta ce a sake bude makrantu a ranar Litinin 18 ga watan Janairu, biyo bayan sake kulle makarantun da aka yi sakamakon barkewar korona a zango na biyu.
“Duk da gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 18 ga Janairu a matsayin ranar bude makarantu, amma jihar Kaduna har yanzu ba ta ayyana ranar budewa ba.”
Ta kara da cewa, har zuwa yanzu gwamnatin tana duba yanayin halin da ake ciki, kana sun bada tabbacin sanar da jama’a da zarar an dauki wani mataki akasin wannan.
“A ranar Litinin 18 ga Janairu ma’aikatar ilimi za ta gana da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi a jihar Kaduna. Sannan, ma’aikatar lafiya za ta mana bayani kan halin da ake ciki dangane da kesa-kesan korona domin baiwa gwamnati shawarorin da suka dace ta dauka nan gaba,” inji ta.
Ta ce, kwalejin KadPoly da jami’ar karatu daga gida ne kawai aka amince musu su bude bisa rokon da suka yi na neman zana jarabawa zalla da aka ba su dama, ta kuma ce sauran manyan makarantun jihar su jira har zuwa lokacin da gwamnati za ta dauki mataki na gaba kan lamarin bude makarantun.