Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Hauwa Inuwa Ta Shawarci Gwamnatin Gombe Kan Hana Sana’ar Acaba

Published

on

A lokacin da ake ci gaba da daukar matakan kariya na hana yaduwar cutar korona bairos a jihar Gombe a shekaran jiya Litinin ne da yammaci gwamnatin jihar Gombe ta fitar da wata sabuwar doka ta hana sana’ar achaba a duk fadin jihar biyo bayan samun rahoton yan Baburan suna fasinja daga Gombe zuwa Bauchi wanda hakan zai iya kawo yaduwar cutar.
Dokar wacce ta shafi masu Keke Napep ma da aka ce ba za su dauki fasinja fiye da guda daya a Keken ba saboda bada tazara tsakanin fasinjoji wanda zai taimaka wajen rage yaduwar cutar.
A lokacin da aka fitar da wannan Dokar ta hannun Mai taimakawa gwamna kan harkokin yada labarai Isma’ila Uba Misilli, Hajiya Hauwa Muhammad Inuwa Gombe, yar rajin kare hakkin dan adam ta kira taron yan jarida inda ta bayyana cutar da cewa gaskiya kuma yan achaban suyi hatta sannan kuma su yiwa gwamnati biyayya.
Hajiya Hauwa Muhammad Inuwa Gombe, tace sa wannan dokar ba’an yi bane dan a hana su cin abinci an saka ta ne dan gujewa yaduwar cutar wanda cikin sauri za ta iya yaduwa idan ana cudanyuwa da juna ta hanyar hawa baburan haya.
Ta kuma bayyana cewa jama’a su kiyaye dokar wanda idan aka samu saukin lamarin za’a iya dage ta a cikin kankanin lokaci idan kuma ba’a kiyaye ba za ta iya daukar tsawon lokaci.
A cewar Hajiya Hauwa Inuwa, daga lokacin da aka haramta wannan sana’ar ta achaba Allah ne kadai yasan adadin gidajen da ba za’a ci abinci ba saboda mafi yawancin yan achaban nan da ita suka dogara wanda sai sun fita su samu abunda za su ciyar da iyalan su.
Ta ci gaba da cewa gwamnati ta tallafa musu tunda duk suna da rijista kuma sun kai fiye da dubu talatin a jihar da suke biyan haraji inda ta wajen su kadai ana samun kudin shiga mai yawa wanda ko dan haka ma ya dace gwamnati ta dube su dan ta rage musu radadin zaman rashin abin yi.
Sannan sai Hajiya Hauwa Inuwa ta kara bai wa gwamna Inuwa Yahaya shawarin ya yi zama da shugabanin yan achaban dan ganin yadda za a taimaka mu su tunda masu karamin karfi ne da sai sun fita sannan za’a ci a gidajensu.
Daga nan sai ta sake yin kira ga gwamnati da cewa kamata yayi kafin daukar matamin doka irin haka nan gaba zai fi kyau a dinga bai wa jama’a dama dan shiryawa saboda yanayin rayuwa dan su san irin shirin da za suyi a gidajen su musamman ma a irin wannan lokaci na bala’in korona ga tsadar rayuwa a lokacin azumi da kashe kudi karuwa ya ke yi kuma kudin basa samsuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: