Connect with us

LABARAI

Korona: Jami’ar KASU Ta Dakatar Da Ma’aikatanta Na Wucin Gadi

Published

on

Jami’ar jihar Kaduna, KASU ta bada umurnin ma’aikatanta wadanda dama ba na dindindin bane da su tafi hutun dole sakamakon cutar Korona ba tare da ta biya su ba.

Magatakardar Jami’ar, Samuel Manshop, shi ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya sanyawa hannu a ranar Alhamis a Kaduna, inda ya ce wannan hutun dolen ga ma’aikatan zai fara aiki ne daga 1 ga watan Mayun 2020.

Sai dai ya tabbatar musu da cewa albashinsu da aka rike har na tsawon wata biyu wato  watannin Maris da kuma Afrilun 2020, za a biya su da zarar Jami’ar an kasonta ya zo hannunta.

Sai dai Samuel Manshop ya tabbatar musu da cewa za a sanar da su ranar da za su dawo daga wannan hutun na dole.

A karshe ya nemi da su mika dukkanin wani abu da suka sani cewa mallakin Jami’ar ne dake hannunsu ga Daraktan sashen lura da lafiya na Jami’ar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: