Abubakar M Tahir" />

Korona: Jihar Jigawa Ta Tabbatar Da Kamuwar ‘Yan Hidimar Kasa 8

Jihar Jigawa

Kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar Korona na jihar Jigawa ya ce a yanzu haka akwai masu yi wa kasa hidima su takwas da aka killace a cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Dutse.

Sakataren kwamitin, kuma babban Sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, Salisu Mu’azu ya sanar da haka ga manema labarai Jim kadan bayan kammala taron kwamitin a Dutse.

Dr. Salisu Ma’azu ya ce masu yi wa kasa hidimar daga cikin guda 11 da aka tabbatar sun kamu da cutar Korona a lokacin karbar horon sanin makamar aiki, ya kuma ce cikin mutum 14 da aka samu da cutar 3 sun warke.

Dr Salisu Mu’azu ya kara da cewa an sake samun wasu masu yi wa kasa hidima su 15 da aka turo jihar Jigawa karbar horan dauke da birbashin cutar Korona, inda su ma tuni aka daukin samfurinsu domin yin gwaji.

Ya jaddada cewa za su bude cibiyoyin kula da masu cutar na Jahun, Birnin Kudu da na Dutse domin kai agajin gaggawa.

Ya dada da cewa, kwamitin yana wani shiri na musamman wanda nan gaba kadan za su fita gangamin wayar da kan al’umma kan wannan cutar.

Ya kuma bukaci al’ummar da su ci gaba da kulawa da dokokin da aka gindaya na kare kai daga wannan cutar.

Gwamnan Jigawa Ya Bada Umarnin Gaggawa Na Rufe Makarantun Jihar

Daga Abubakar M Tahir Hadejia

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya bada umarnin gaggawa na garkame duk akarantun Firamare da na Sakarandare mallakar Jihar da na masu zaman kansu.

Gwamnan ya fitar da sanarwar ne ta hannun Babban Sakataren ma’aikatar ilimi ta Jihar Jigawa, Alhaji Rabiu Adamu da aka rufe makarantu tun a ranar Talata 15/12/2020, kuma za a rufe su ne har sai baba-ta-gani.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya dauki wannan matakin ne tun bayan da mahara suka afka makarantar Kwana da ke kankara ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 600.

Jihar Jigawa jiha ce da ke makwaftaka da Katsina ta Yankin Kazaure.

Exit mobile version