Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Kada Ku Manta Da Marayu – Dr. Halima Ga Buhari Da Ganduje

Published

on

An tunawa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Da Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje da kada su manta da halin da al’ummarsu su ka shiga, musamman marayu da sauran marasa galihu a lokacin wannan annoba ta cutar Korona, wacce ta haddasa kulle mutane a gida da Shugaban kasa da gwamnoni su ka yi a matakai daban-daban, don yakar annobar.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin wacce a ke yi wa lakabi da Uwar Marayu, Dr. Halima Usman Abdullahi, kuma shugabar makarantar FarmaLanda Group of Schools da ke Kano a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai ranar Alhamis din da ta gabata.
Har ila yau ta ce, “kullen jama’a a gida ga azumi wannan ya jawo matsala, musamman ma dai ga marayu, wadanda da ma ba su da wani mai taimaka mu su sai Allah da kuma wasu bayin Allah da ya zaba ya sa wa wannan aiki na taimako. To, kuma sai a ka ce an kulle gari; ba shiga ba fita, duk makarantunmu da a ke biyanmu kudi mu dan ajiye wani, don mu talafa wa marayu bayan mun biya ma’aikatanmu, babu. Saboda haka wannan ya zama sababin matsala gare mu da marayunmu.”
Dr Halima Uwar Marayu kuma shugabar kungiyar Kumbotso Marayu, ta ce, ita a matsayinta malamar makaranta ta na taimaka wa marayu da tallafi a duk azumi na akalla marayu 200 da abinda ta samu na makaranta da abinci da sauran tallafi da kuma wanda ta ke samu daga wasu kungiyoyin jin kai, irinsu Gatan Marayu da irinsu Alfurkan Ramadan Trust da dai sauran kungiyoyi kamar hudu, wadanda su ka taimaka wanda abin a yaba mu su ne kwarai da gaske, ta ce, wannan taimako nata da na kungiyoyi ne a ka samu a ka rika tallafawa da abinci.
Ta dauki mota ta na bi gida-gida da cibiyoyin marayu ta na kai mu su tallafin, wanda akalla marayu 100 su ka amfana maimakon 200 da su ka saba taiamakawa a duk irin wancan lokaci na azumin Ramadan.
Dr Halima Uwar Marayu ta ce kuma, wani abin mamaki shi ne, ta ji a na maganar taimako daga Gwamnatin Kano da ta Tarayya, amma ita dai shugabar kungiyar babu wanda ya neme ta da sunan bayar da taimako.
Ta ce, “ko su marayu ba su da hakki a wannan taimako ne na gwamnati? To, idan su na da hakkin su ma su na da bukata a ba wa kungiyoyin marayu irin nasu ko da ba su ba, a ba wa duk wani wanda ya cancanta a bawa, to a ba shi; ba sai mu kawai ba.
Dr Halima Uwar Marayu ta cigaba da cewa, “wannan shi ne kirana ga Gwamnan Kano da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan su tuna da halin da al`umma ta ke ciki na matsi da talauci, musamman dai marayu da sauran marasa galihu a kasa.”

Advertisement

labarai