Connect with us

LABARAI

Korona: Kano Ta Dauki Dumi

Published

on

  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Mu, In Ji Ganduje
  • Ku Ma Na Garkame Ku, Cewar Buhari
  • Kano Ta Rasa Mahimman Mutane 12 Cikin Awa 10 Kacal
  • Maleriya Ke Kashe Kanawa Ba Korona Ba – Kwamishina

Jihar Kano ta na cigaba da samun mace-macen da su ka saba wa al’ada a daidai lokacin da akalla wasu mahimman mutanan Jihar 12 a ka tabbatar da rasuwarsu a ranar Asabar da ta gabata. Muhimman mutanan kuwa sun hada har da wasu manyan farfesoshin Jihar, wani babban editan jarida da sauran manyan mutanen jihar.

Duk kuma an binne su ne a makabartu daban-daban a ciki da wajen birnin na Kano.

A cikin dai kwanaki Takwas da kafa dokar hana zirga-zirga a Jihar ta Kano, akalla mutane 20 ne suka rasu a sabili da wasu ciwukan da ba a tantance su ba.

Daga cikin mahimman mutanan Jihar da suka rasu a ranar ta Asabar akwai Farfesa Ibrahim Ayagi, Dakta Musa Umar Gwarzo, Alhaji Dahiru Rabiu (tsohon alkalin alkalan Jihar), Musa Tijjani (Editan Jaridar Triumph) da Adamu Isyaku Dal, wanda shi ne tsohon Sakataren hukumar ilimin bai daya ta Jihar.

Sauran sun hada da Alhaji Salisu Lado, Hajiya Shamsiyya Mustapha, Hajiya Nene Umma, Alhaji Garba Sarki Fagge, Dakta Nasiru Maikano Bichi, Sakataren harkokin dalibai, a Jami’ar arewa maso Yamma, Farfesa  Aliyu Umar Dikko na Jami’ar Bayero Kano, da mahaifiyar Ado Gwanja da sauransu.

Yawan mace-macen dai da ke aukuwa a Jihar ta Kano yana jefa tsoro da firgici a zukatan mazauna Jihar.

Wani mazaunin Jihar mai suna, Tijjani Abdullahi, da ya zanta da wakilinmu ya yi kira ne ga gwamnatin Jihar da ta binciki karuwan yawan mace-macen a garin na Kano domin gano dalilinsa.

A cewarsa, yawancin mace-macen ana alakanta su ne da hawan jini, zazzabin maleriya, Ulsa da kuma yunwa, ya kara da cewa, hakanan mutuwar Likitocin da ya kamata a ce su ke duba marasa lafiya a Asibitocin Jihar shi ma babban abin damuwa ne.

Sai dai kuma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Laraba ya musanta cewa ana wani yawan mace-mace a cikin Jihar, yana mai cewa, “Sam babu wani abin da ke nuna cewa ana yawan mace-macen da suka saba wa ka’ida a Jihar Kano.”

A yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan halin da jihar ke ciki kuwa, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya zargi kwamitin ko-ta-kwana da Shugaban kasa ya kafa a kan yaki da annobar Korona, da yin watsi da Jihar ta Kano a bisa kokarin da Jihar ke yi na yakar annobar.

Ganduje ya bayyana rashin jin dadin na shi ne cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na gidan rediyon BBC ya yi da shi a ranar Litinin.

Gwamna Ganduje ya ce, “Muna cikin matsala sosai, Ina gaya maka, matsalar tana da ban tsoro. Domin abin da muka dogara kacokam a kansa domin yaki da annobar shi ne cibiyoyin gwaje-gwaje.

“Akwai kuma karancin kayan daukan gwajin. Ba kuma kaya ne da za ka iya zuwa kasuwa ka siyo su ba. Wadanda ma aka dauki gwajin na su har yanzun suna nan suna ta jira ne domin su ji sakamakon su.

“Duk matsalar kuma ta Kwamitin na Shugaban kasa ne, hatta babban daraktan Kwamitin ya zo nan Kano. Ya kwana guda, amma tun da ya tafi ba mu sake jin wani abu ba daga gare shi. Ma’aikatar lafiya ma tana sane da cewa dakin bincike da gwaje-gwajenmu ba ya yin aiki.

“Akwai fa babbar matsala. Muna ta kai kukan cewa Kano tana da bukatar wajen bincike sama da guda daya, tun farkon barkewar annobar.”

Yayin da gwamna Ganduje ya ke amsa tambayar ko Jihar ba ta sami taimakon komai ne ba daga hukumomin na gwamnatin tarayya domin yakar annobar ta Korona. Sai Gwamna Ganduje ya ce, “Maganar gaskiya, sam ba ma samun taimakon da ya kamata. In da a ce muna da wadannan cibiyoyin binciken, tabbas da mun yi bakin kokarinmu mu ga suna yin aiki yanda ya kamata. Amma matsalar ita ce sam ba ma samun taimakon da ya kamata da hadin kai daga Kwamitin na shugaban kasa a kan yaki da annobar ta Korona.

Sai dai kuma, Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya fada a cikin wani shiri da aka yi da shi ranar Lahadi a tashar talabijin ta Channel, cewa cibiyar binciken ta Kano za ta fara aiki ne a ranar Litinin (jiya kenan), ya kara da cewa za a aike da wata tawaga a can Kano din domin su binciki dalilin yawaitar mace-macen da ake samu a jIhar ta Kano.”

Shi kuwa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke gabatar da jawabi kan annobar cutar ta Korona da ya saba yi duk bayan makonni biyu ya bayyana cewa, zai garkame jihar bakidayanta, don tabbatar da cewa, an kawo karshen yaduwar cutar.

A ta bakin shugaban, duk da cewa, za a sassauta wasu matakan a wasu jihohi, amma Jihar Kano lamarinta zai sha bamban, domin za a yi ma ta cikakken kulle a tsawon makonni biyu masu zuwa.

To, a wani cigaban kuma, Gwamnatin Jihar Kano ta ce, yawaitar mace-macen da a ke samu yanzun haka a jihar ya na faruwa ne a dalilan cutukan hawan jini, ciwon sukari da zazzabin maleriya mai zafi.”

Kwamishinan yada labarai na Jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi da dare.

Kwamishinan ya ce, “Duk da cewa har yanzun ana ci gaba da gudanar da bincike a kan musabbabin yawaitar mace-macen da ake yi a birnin na Kano, amma dai sakamakon farko daga ma’aikatar lafiya ta Jihar ya yi nuni da cewa ko kusa mace-macen ba su da wata alaka da annobar Korona. Rahotanni sun nuna cewa yawancin mace-macen suna aukuwa ne a sabili da cutukan da suka shafi hawan jini, ciwon sukari da kuma zazzabin maleriya mai zafi.”

“A yanzun haka dai, Jihar ta Kano tana da cibiyoyi har uku na zamani domin gwajin masu dauke da annobar ta Korona, wajen kuma da ake ci gaba da kula da su. muna kuma sa ran samun karin wasu wuraren biyu domin kebe masu dauke da cutar ta Korona nan ba da jimawa ba. gwamnatin Jihar ta kuma yi hayan wani hotal inda ake ci gaba da kulawa da wadanda ake zaton suna dauke da cutar ta Korona.

“Hakanan, Gwamnatin ta Jihar Kano tana hada kai da Jami’ar Bayero domin kafa wata cibiyar binciken a cikin Jami’ar wacce ake sa ran kammala ta a cikin makwanni biyu a bayan da hukumar ta NCDC ta amince da sahihancin ta. Wanda hakan zai taimaka matuka wajen tabbatar da gwada duk wani da ake kyautata zaton yana dauke da cutar ta Korona.

A cewar cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC, kamar yanda cibiyar ta fada a ranar Lahadi da dare, akalla mutane 77 daga cikin 1273 da aka tabbatar suna dauke da cutar ta Korona a cikin kasar nan duk daga Jihar ta Kano ne suka fito.

Ma’aikatar lafiya ta Jihar ta ce, har yanzun babu wani da ya warke a Jihar tukunna, ma’aikatar ta kuma ce mutum guda ne kadai aka tabbatar da mutuwarsa a sakamakon cutar ta Korona a cikin Jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: