Abdullahi Muhammad Sheka" />

Korona: Kano Ta Yi Watsi Da Bukatar Garkame Makarantu

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, ta yi watsi da shawarar da kungiyar na ta sa kai, yada labarai da cigaban fasaha (CITAD) ta bukata ta sake garkame makarantun jihar.

Da ya ke tsokaci kan wannan batu, Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Kano, Malam Muhammad Sunusi kiru, ga manema labarai jiya a birnin Kano, cewa ya yi, gwamnatin jihar ba ta tsara sake rufe makarantu ba sakamakon annobar Korona.
Hon. kiru ya ce, bayan kyakkyawan shirin sashen bibiyar al’amuran, Gwamnatin Tarayya ma na kara sai ido, domin lura da yadda ake bin ka’idojin matakan kariya ga cutar ta Korona kuma basu ga laifin Gwamnatin Jihar Kano ba akan haka.
“Abinda mu ka yi zato a matsayinku na masu sa ido, za ku tuntube mu kan binciken da kuka gudanar a makarantun mu kafin yiwa manema labarai bayani, kawai sai ku yi kira da a rufe makarantun sakamakon bincikenku. Yin hakan ba ku yi wa sashen ilimi adalci ba.”
Kan batun cinkoso a makarantu kuwa, Kwamishinan cewa ya yi, ya kamata a yi la’akari da shirin Gwamnatin Jihar Kano na batun ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa.
“A bayyane lamarin yake,  kamar yadda kuka sani an samu karuwar yaran da ake shigarwa makarantu ga kuma batun gina makarantu ko gyaransu lamari ne da akeyi Shekara Shekara, abune da ake shigarwa cikin Kasafin kudi, ana fatan samar da kudade na gaba kadan.
“Jihar Kano keda yawan dalibai a fadin kasarnan wanda sakamakon haka dole muyi la’akari da abinda ake da bukata cikin gaggawa.”
Gwamnatin Jihar Kano data rufe Makarantu zuwa wasu watanni nan gaba sakamakon karuwar cutar Korona.
Idan za a iya tunawa, a shekaranjiya ne, kungiyar CSO, ta yi taron manema labarai, inda take sukar Gwamnatin Jihar Kano, tana mai cewa, ba ta samar da isassun matakan kariya da za su iya dakile yaduwar annobar Korona dake yaduwa a makarantun ba bayan sake bude makarantun a watan da ya gabata.
Jawabin haka ya fito daga bakin jami’in tsare tsare na kungiya CITAD kan matakan kariya daga annobar Korona, Ali Sabo, ya bayyana damuwarsa bisa karya matakan kariya a mafi yawan makarantun Jihar Kano, musamman ajujuwa da suke cimkoson dalibai, don haka babu damar da samar da tsarin tazara.
Kamar yadda aka gani a ranar Lahadi 31 ga watan Janairun Shekara ta 2021 kadai an samu karuwar mutane 40 da suka kamu da cutar tare da samun mutuwar mutane biyu.
Ali Sabo ya ce, sakamakon kididdigar da kungiyar CITAD ta gudanar kan matakan kariya ga Annobar Korona a wasu makarantu, an tabbatar da cewa da yawa makarantun basu shirya Ingantaccen shirin sake bude makarantun ba.
“Abin mamakin shi ne Gwamnatin Jihar Kano ta umarci ma’aikatan Gwamnati su zauna a gidajensu sakamakon sake bullar annobar Korona zagaye na biyu, amma banda makarantu, ana ganin ofisoshi nada yawan Mutane kamar yadda suke da yawa a ajujuwa? inji Sabo.
“Damuwarmu ita ce yadda ake samun karuwar masu kamuwa da kuma mace mace a Jihar Kano da kasa baki daya.”
kungiyar ta CITAD ta shawarci Gwamnatin Jihar Kano da ta kara samar da tsare tsare a makarantun Gwamnati domin magance matsalar cinkoso a ajujuwa da dakunan kwanan dalibai.

Exit mobile version