Connect with us

RAHOTANNI

Korona: Karin Mutum 575 Sun Kamu A Nijeriya

Published

on

An sake gano mutanen da suka kamu da cutar korona 575 ranar Alhamis, yawan mutanen da cutar ta shafa sun kai 31,323.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fada cikin bayanan da ta fitar a daren Juma’a cewa masu korona 20 sun mutu cikin sa’a 24.

NCDC ta kuma ba da rahoton cewa mutum 249 sun warke daga cutar har ma an sallame su daga cibiyoyin killace masu korona.

Zuwa yanzu adadin masu korona da suka warke 12,795, wato kasa da rabi na illahirin masu cutar da hukumomi suka gano.

Hakan ya nuna akwai masu cutar korona 18,528 da ke kwance a cibiyoyin kwantar da masu cutar, inda suke ci gaba da jinya.
Advertisement

labarai