Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Korona: Kashi 74.2 Na Harkokin Kasuwanci Ya Tsaya Cik – NECA

Published

on

Kungiyar ma’aikata masu bayar da shawarwari ta Nijeriya (NECA) ta bayyana cewa, binciken da ta gudanar a kwanan nan ya nuna cewa, kashi 74.2 na harkokin kasuwanci a cikin kasar nan sun tsaya cik, sakamakon cutar Korona. Mukaddashin shugaban kungiyar NECA, Taiwo Adeniyi, shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a Jihar Legas. Haka kuma ya bayyana cewa, kashi 15.8 na haerkokin kasuwanci ko dai sun ci gaba da gudanar da kasuwancinsu yadda suka saba ko kuma sun yi kasa.

“Sama da kashi 90 na kamfanoni sun samu karancin kudade wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu sakamakon cutar Korona, yayin da sama da kashi 90 na masu sayan kayayyaki da ayyuka suka ragu. Kamfanoni sun fuskanci matsaloli wajen rarraba kayayyaki wanda ya kai na kashi 78.2,” in ji shi.

Ya yaba wa gwamnatin a kowani mataki wajen kokarin dakile yaduwar wannan cuta na Korona a cikin kasar nan. A cewarsa, samar da harkokin kudade na tallafin Korona a kan harkokin kasuwanci, ya farfado da tattalin arziki daga durkushewa. Ya ce, lallai harkokin kasuwanci ya fuskanci matsanancin hali a lokacin cutar Korona.

“An rufe mafi yawancin harkokin kasuwanci, yayin da mafi yawanci suka talauci, muna kira ga gwamnati da ta tallafa wa harkokin kasuwanci, wajen tabbatar da cewa ya sake farfadowa daga wannan durkushewan da ya yi.

“An samu karuwar rashin aikin yi lokacin cutar Korona. Harkokin kasuwanci yana samar wa dinbin mutane ayyukan yi a cikin kasar nan.

“Haka kuma an samu matsaloli masu yawa daga cikin ayyukan tattalin arziki lokacin wannan cuta. Domin haka ne muka bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen tallafa wa harkokin kasuwanci, domin zai bayar da damar farfado da tattalin arziki a cikin kasar nan,” in ji shi.

Mista Adeniyi ya yi kira ga babban bankin Nijeriya da ma’aikatar kudi da hukumar da ke tattara haraji ta Nijeriya da sauran hukumomi da su aiwatar da da wani tsari a kan harkokin kudade.

Ya ce, “wannan tsari zai bayar da damar bunkasa duk wata fanni na tattalin arziki da ke cikin kasar nan, sannan zai samar da ayyukan yi da janyo ra’ayin masu zuba jari wanda zai sa su zuba dinbin jari a kan wani fannin tattalin arziki da kuma bunkasar harkokin kasuwanci a cikin kasar nan. Lallai wannan tsarin zai taimaka wa kasar nan wajen farfado da tattalin arzikinta wanda ya durkushe sakamakon barkewar cutar Korona. Ina fatan gwamnati zai ta yi amfani da wannan shawarwari da muka bayar domin inganta harkokin kasuwanci a cikin kasar nan.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: