- –Umarnin Kotu Ga Gidan Yarin Kaduna
Daga Rabiu Ali Indabawa,
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta umarci mahukuntan gidan yari dake Kaduna da su gaggauta mika Malama Zeenat, matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, jagoran mabiya dari’ar Shi’a a Nijeriya, zuwa cibiyar killace mutane, domin a duba lafiyarta bayan da bayanai suka nuna cewar ta kamu da cutar Korona.
A makon jiya ne Mohammed, dan Sheikh El-Zakzaky, ya sanar da cewa, mahaifiyarsa, Malama Zeenat, ta kamu da cutar ta Korona, amma an hana fita da ita zuwa cibiyar killacewa.
Lauyan Sheikh El-Zakzaky, Femi Falana, ya gabatar da sakamakon gwajinta na takardun asibiti da suka nuna Malama Zeenat din na bukatar kulawa, saboda yanayin lafiyarta.
A hukuncin da ta yanke ranar Litinin, kotun ta bayar da umarnin a gaggauta mayar da Zeenat zuwa cibiyar killacewa mallakar gwamnati, domin ta fara karbar maganin cutar Korona.
Tun a shekarar 2015 gwamnati ta tsare Sheikh El-Zakzaky tare da matarsa biyo bayan wata arangama a tsakanin magoya bayan Shi’a ta IMN da dakarun rundunar soji a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Femi Falana, lauyan El-Zakzaky kuma Babban Lauyan mai lambar ‘SAN’, ya roki kotun ne don ta yi la’akari da shaidun da ya gabatar wajen bayar da wancan umarni na sakin Zeenat din, domin ta samu kulawa a cibiyar killacewa kamar yadda hukumar NCDC mai yaki da cututtuka ta tsara tun bayan barkewar annobar Korona a duniya.