Connect with us

RAHOTANNI

Korona: Kungiyar FONWAN Ta Dukufa Wajen Wayar Da Kan Alumma A Katsina

Published

on

Kungiyar da’awa mata hadin gyuwa da FONWAN , sun dukufa wajen wayar da kan mata , akan cutar Korona, da ta hana mutane sakat a fadin diniya.
Shugabar kungiyar da’awa mata reshen jihar Katsina, Hajiya Halima Muhammad Lailu Funtua, ce ta bayyana haka a lokacin ta taron wayar da kan mata a karamar hukumar Funtuwa.
“Hajiya Halima Lailu ta bayyana cewa, “wannan tagwayan kungiyoyi sun dukufa wajen wayar da kan mata a fadin jihar Katsina, tun kafin annobar ta yi kamari, ta jawo kule wasu kananan hukumomin a yanzu haka.
‘Kuma kungiyar da’awa da ta Famwan karkashin jagorancin shugabarta ta jihar Katsina, Hajiya Safiya Usman Nagogo, muka raba kanmu zuwa sasan bangarorin yakunan jihar Katsina, muka shiga lunguna da sako don wayar da kan ‘yan uwa mata akan yadda za’a kauce ma samuwar wannan anobar cutar.
‘Hajiya Halima Lailu ta kara da cewa, sanin kuwa ne mata sune jigon rayuwar alumma, kuma su ke tare da yaran su a kodayaushe dan haka muka fadakar da su wajen inganta tsaftace muhalin su dan tsafta cikoce ta imani, kamar yadda yazo a cikin hadisan manzan Allah (swa ) kuma rashin tsafta na jawo samuwar wannan annoba.
‘Akan haka ne muke zagayan wayar da mata kan tsatace, hannayan su da kuma yin amfani da sinadarin goge hannun da sabulun wanke hannu .kuma mun bada su kyauta ga su matan .
“Kuma wannan kungiyoyi namu ba karkashin gwamnati su ke ba ,kungiyoyin ne masu zaman kansu kuma da dan abubuwan da ke hannun mu muke amfani da su wajan wayar da kan ‘yan uwan mu mata .
“Dan haka mu ke kira ga gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari da tasanya kungiyoyin Da’awa mata da ta Famwan cikin dukkan wani kwamitin na wayar da kan alumma da fadakar da su kan duk kan abubuwan cigaban rayuwar alumma.
‘A karshe Hajiya Halima Lailu ta yi kira ga ‘yan uwa mata da suji tsoran Allah wajan tafiya da rayuwat su , da kuma bin shawarwarin Ma’aikatan Lafiya dan rigakafin kamuwa da wannan Annobar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: