Khalid Idris Doya" />

Korona: Ma’aikatan Bauchi Sun Zargi Gwamnati Da NLC Da Hadin Baki

Ma’aikatan gwamnati a jihar Bauchi sun zargi kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar kan hada baki da gwamnatin jihar Bauchi domin zaftare mu su wani kaso daga cikin albashinsu da sunan yaki da cutar Koronabairus.

LEADERSHIP ta nakalto cewar a kwana-kwanan ne gwamnatin jihar ta sanar da cire kashi 1 cikin 100 na albashin kowani ma’aikaicin gwamnati da ke jihar mai matakin aiki daga 1 zuwa 15 domin taimaka wa gwamnatin wajen yaki da Korona na tsawon wata uku.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakin Gwamnan Bauchi, Muktar Gidado ya fitar a kwanan nan, ya shaida cewar gwamnati ta cimma matsaya da cimma matsayar da NLC kan zaftare kason albashin ma’aikatan.

A cewar sanarwar, a bisa yarjejeniyar da aka tsaida matsaya a kai, manyan sakatarorin dindindin na ma’aikatun jihar zuwa sama sun sadaukar da kashi goma cikin dari na albashinsu na watan Afrilun, Mayu, da kuma wayan June na 2020.

“Sai kuma Daraktoci masu matakin aiki na 16 zuwa 17 na ma’aikatan Bauchi da kananan hukumomin jihar sun bada kaso 5 na albashinsu na tsawon watanni uku,”

Sai dai wasu manyan ma’aikatan gwamnatin jihar da suka gana da jaridar nan sun zargi reshen NLC na jihar da yin gaba-gadi ba tare da tuntubar ma’aikata ko jin ra’ayinsu ba, sun nuna cewar kawai sun ji batun zaftare musu albashin tare da ganin hakan a zahirance ba tare da wani bayani ba.

“Babu wanda aka nemi shawararsa ko aka tuntuba da irin wannan batun zaftare albashin da suka yi. Kawai dai sun gayyaci NLC tare da basu toshiyar baki domin su mika ma’aikatan jihar bori ya dale,” A cewar wani babban darakta na wata ma’aikata a jihar da ya bukaci mu sakaye sunanshi.

Daraktan ya kara da nuna nadamarsu da salon shugabancin kungiyar NLC, inda ya ce babu wani da zai sake daddara da su ko ya sakankance kan cewar za su nema masa hakkinsa, inda ya kara da cewa fatansu ya kare da su.

“Kalli batun sabon tsarin albashi mafi karanci yanda suka shiga daki suka sasanta a tsakansu shi kenan batun ya sha ruwa shiru kake ji;” sai ya zargi kungiyar da amsar na goro tare da jingine bukatun ma’aikatan jihar a gefe a maimakonsu su tsaya kai da fata domin kare musu muradunsu.

Wani ma’aikacin gwamnati daga karamar hukumar Gamawa da ya gana da wakilanmu, ya shaida cewar hatsarin da ke cikin zaftare albashin ma’aikata da suna yaki da Koronabairus hatsari ne babba ga siyasar gwamnati mai ci, sai ya nemi gwamnatin da ta yi hattara domin zabe na gaba.

“Ma’aikatan gwamnatin Bauchi suna da yawan da kuri’unsu na gayar tasiri a lokacin zabe, ga iyalanmu mata ga ‘ya’yanmu da makusanta, don haka ma’aikata a Bauchi ba abin wasa da jin dadinsu ba ne.”

Sai ya bukaci gwamna Bala Muhammad da ya gaggauta sauya wannan matakin lura da bukatar da hakan ke da shi ko don kimarsa, “Mu na da masu rike da mukaman siyasa da suka hada da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi, meye sa gwamnati ba ta bukaci tallafi daga garesu ba sai kawai ta dira kan albashin ma’aikatan jihar? Ya dace ne ta nemi tallafin kudade daga wajen masu rike da mukaman siyasa da ‘yan majalisu da sanatocin jihar domin ci gaba da yaki da cutar nan,” a cewarshi.

Ma’aikacin ya kara da cewa, “me ya sa su ka mance da talakawan ma’aikata da su ke rayuwa da dan albashin da su ke samu a duk wata,” ya tambaya.

Ya nuna damuwarsa bisa yanda NLC ta amince da bukatar gwamnatin ba tare da jin ra’ayoyinsu ba, ya nuna hakan a matsayin gazawar shugabanninsu tare da farkar da su kan cewar su yi kokarin sauya halayensu domin gudun abin da ka iya jewa ya zo.

“Da wa su ka yi shawara? Shi ba mu cancanci su tuntubemu kafin su amince da daukar irin wannan matakin a madadinmu ba?,” ya dage.

Wani ma’aikacin gwamnati a cikin karamar hukumar Bauchi ya nuna mamakinsa da yanda NLC suka kasa nemo musu hakkokinsu amma sun iya daukar hanya su mika wuyan ma’aikata don sallamasu ba tare da jin ra’ayinsu ba.

Sai kuma ya shaida cewar da bukatar dai a duba halin da ma’aikata suke ciki, “A irin wannan lokacin ma’aikata ya kamata a fi taimakama wa ba wai a rage musu albashi ba. Gwamnati ai da fadi take ta nemo kudadenta daga wasu hanyoyin mana,” A cewar shi.

Duk kokarin da wakilinmu yayi don jin ta bakin shugaban kungiyar kwadago NLC reshen jihar Danjuma Saleh abun ya citura har zuwa aiko da wannan rahoton, idan mun samu ji ta bakinsa za mu buga.

Sai dai kamar yanda sanarwar gidan gwamnatin ya shaida ta bakin Gidado sun ce, dukkanin bangarorin da abin ya shafa sun rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar yin hakan, inda ya ce shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Ahmed Ma’aji, Shugaban kungiyar gamayyar ‘yan Kwadago a jihar NLC, Kwamared Danjuma Saleh, Shugaban kungiyar Trade Union Congress TUC, Kwamared Sabi’u Muhammad Barau tare da Shugaban Joint Public Serbice Negotiation Council, Kwamared Dauda Shuaibu dukkaninsu sun tattaba hannu kan yarjejeniyar tare da amincewa da shi.

Exit mobile version