Mahdi M Muhammad" />

Korona: Maganin Riga-kafi Na Jabu Na Yawo – NAFDAC Ta Yi Gargadi

NAFDAC

A jiya Juma’a ne hukumar kula da abinci da magunguna (NAFDAC) ta sanar da yaduwar riga-kafin korona na jabu a Nijeriya duk da cewa ta bayyana cewa ba ta amince da kowane irin riga-kafin ba daga masana’antun riga-kafi na cikin gida.

Hukumar ta kuma yi gargadin amfani da duk wani maganin riga-kafi ba tare da amincewar hukumar ba.

Da take bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta ce, “Alurar riga-kafin ta korona sabuwa ce, kuma dole ne a lura da illolin ko kuma abubuwan da za su haifar, don haka, idan NAFDAC ba ta yarda ba, bai kamata jama’a su yi amfani da shi ba.”

“Akwai rahotannin yin allurar riga-kafin karya a Nijeriya. NAFDAC tana rokon jama’a da su kiyaye. Babu wani wani riga-kafin korona da NAFDAC ta amince dashi. Jabun alluran riga-kafin na iya haifar da cututtuka wadanda zasu iya kashe mutane.”

Adeyeye ta lura da umarnin da ba a amince da shi ba na kamfanoni masu zaman kansu da hadin kai ta ce, “Bai kamata wani kamfani ya ba da allurar riga-kafin ba. Kamfanonin da ke kera alluran idan kamfanoni na gaske ne sun san dole ne su gabatar da takardar su ga NAFDAC.”

Ta ci gaba da cewa, babu wata kafa ta gwamnati ko hukumomi masu zaman kasu da za su ba umarnin a yi allurar riga-kafin ba tare da tabbatarwa daga NAFDAC ba idan an amince da allurar.

“Haka zalika, NAFDAC na tattaunawa da masu kera alluran riga-kafin korona game da yiwuwar amfani da agajin gaggawa (EUA), rajista ko lasisin samfurin su kamar yadda lamarin yake. Hukumar ta ba masu neman izinin cewa idan har gwajin 3 sunyi kyau za a tabbatar da karfi game da aminci da ingancinsa, kuma an gabatar da allurar riga-kafin ga WHO don lissafin amfani da gaggawa, NAFDAC za ta yi maraba da aikace-aikacen neman izinin amfani da gaggawa a Nijeriya.”

Exit mobile version