Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Majalisar Malamai Ta Yi Kira Ga Musulmi Su Dukufa Da Addu’a

Published

on

An Shawarci al’ummar Musulmi da suyi amfani da watan ramadana mai tsarki wajen yawaita addu’oi da neman gafarar Ubangiji domin kawo karshen annobar korona bairos dama sauran bala’oi wadanda suka addabi duniya baki daya.

Majalisar Malamai ta kasa,( Council Of Ulama’u) reshen jihar Kogi ne tayi kiran a wajen bude lakcar azumin watan ramadan data saba shiryawa kowace shekara a babban masallacin juma’a dake garin Lakwaja,babban birnin jihar Kogi.
Majalisar wanda tayi kiran ta bakin sakatarenta na mulki,Alhaji Baba’ango Idris,ta kuma Shawarci al’ummar Musulmi dasu bi umurnin hukumar yaki da cututtuka ta kasa(NCDC) na su rika wanke hannayensu da sabulu da sinadarin wanke hannu(Sanitizer) da nisantar juna da kuma sanya badda kama na fuska(face mask) don kandagarkin annobar cutar cobid 19.
Ta kuma yi kira ga Malamai masu wa’azuzzuka cikin wannan wata mai tsarki da suyi aiki da umurnin Mai alfarma Sarkin Musulmi ,Alhaji Sa’ad Abubakar inda ya bukaci malaman dasu dakatar da wa’azuzzuka da kuma sallar tarawi saboda cutar korona wanda a yanzu sai kara kamari take yi.
Sai dai kuma majalisar tayi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai dasu kawowa talakawa dauki ganin cewa bullar cutar ta korona ta jefa miliyoyin yan Nijeriya cikin halin kuncin rayuwa.
Majalisar wanda tunda farko ta shirya addu’oi na musamman don kawo karshen matsalolin dake addabar kasar nan wadanda suka hada da satar jama’a da matsalar yan bindiga da harkokin kungiyar asiri da kuma na baya bayan nan,wato cuar cobid 19,ta kuma bukaci al’ummar Musulmi musamman masu hannu da shuni dasu rika taimakawa marasa karfi daga cikin dukiyar da Allah Ya hore musu musammama a wannan wata mai alfarma.
Kazalika majalisar tayi kira ga yan kasuwa dasu tausaya su rage farashin kayayyakin masarufi da sauran abubuwan amfani domin talaka ya samu sa’ida.
Cikin wadanda suka halarci bude lakcar sun hada da babban limamin garin Lakwaja, Ustaz Aminu Sha’aban da tsohon alkalin alkalai kotun dauka kara ta addinin musulunci na jihar Kogi,Mai shari’a Suleiman Olorunfemi da Khadi Khalifa Nuruddeen Yusuf Abdallah da limamin masallacin Tudun Natsira, Alhaji Abubakar Ungulu da dai sauran al’ummar daga ciki da kuma wajen Lakwaja.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: