KORONA: Manchester City Ta Soke Wasanta Da Troyes

Manchester

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta soke wasan sada zumunta da zata buga tun farko da kungiyar kwallon kafa ta Troyes, saboda dokar gwamnatin Burtaniya kan killace kai idan aka je kasar Faransa.

Sabuwar dokar hana yada cutar korona a Burtaniya ta tanadi duk wanda zai koma Burtaniya daga Faransa, zai killace kai ba tsawon kwanaki 10, wanda hakan zai shafi shirin kungiyar domin tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta.

Tun farko an tsara kungiyoyin biyun za su yi wasan sada zumunta ranar 31 ga wata Yuli a Faransa kuma wannan labarin ya zo ne, bayan da Manchester City ta sanar cewar za ta yi wasan sada zumunta da Preston ranar 27 – wanda za ta buga ba ‘yan kallo.

Manchester City ta ce za ta buga karawar ba ‘yan kallo a filin makarantar koyon kwallon kungiyar, bayan da aka rufe cibiyar tun 16 ga watan Yuli, bayan da aka samu wasu sun kamu da cutar korona.

Wasan da Manchester City za ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Preston shine na farko tun bayan fafatawar karshe da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a Champions League ranar 29 ga watan Mayu.

Manchester City za ta bude kakar bana da Community Shield da Leicester City a filin wasa na Wembley ranar 7 ga watan Agusta, sannan ta fara wasan Premier da Tottenham ranar 15 ga watan Agusta.

 

Exit mobile version