Connect with us

LABARAI

Korona: Masu Sayar Da Katako A Kano Sun Koka 

Published

on

Shugaban kungiyar masu saida katako da sauran kayayakin gini a Kano wato, ‘Timber & Building Material Sellers` Association Kano, Alhaji Magaji Gambo ya bayyana cewa zuwan cutar korona harkar su ta saida katako ta samu matsala, musammam a lokacin da aka kulle gari bashi ga ba fita hakan ya jawo musu asara mai yawa, saboda katako wani abu ne da yake bukatar kulawa ta yau da kullum ta hanyar juya shi da gyara shi to kuma hakan ba ta samu ba sakamakon kulle gari da gwamnati ta yi a matakai daban- daban domin yaki da cutar.

Magaji Gambo wanda ke tare da sakataran kungiyar Auwalu A. Adamu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana damuwarsa ga manema labarai a ranar jumma’ar da ta gabata, kan abin da ya shafe su na tabarbarewar al’amura sakamakon zuwan Korona kano, da ma duniya baki daya wanda kuma ya roki madaukakin sarki ya kawar da wannan cuta da ta addabi duniya.

Har ila yau ya ce, kafin abubuwa su zama haka suna samun baki daga jahohin makota har da Nijer kafin rufe iyakar kasar mu don haka an samu raguwar abokan ciniki tun kafin Korona to sai ga Korona mastala ta karu a kasuwanin katako don haka suna kira da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan tallafa musu a kan matsalolin da suka samu a wannan lokaci.

A karshe ya bayyana cewa su a mastayin sun a ‘yan kasuwa suna iya kokarunsu na bin dokoki da addu’a domin yakar Korona kamar yadda Gwamnati da jami`an kiwon lafiya da masana suka tsara a yi don yakar cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: